Adamawa: Mutum 50 sun mutu a hatsarin mota

Nigeria hatsari Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Ana yawan samun afukuwar hatsarin mota a titunan Najeriya

Rahotanni daga jihar Adamawa da ke arewa maso gabashin Najeriya na cewa mutane fiye da 50 ne suka rasa rayukansu sanadiyar wani mummunan hadarin mota a kusa da garin Ngurore.

Lamarin ya faru ne a ranar Lahadi da daddare yayin da dumbin mutane cikin babbar motar dakon kaya ke komowa gida daga kasuwar garin Song.

Mutanen da lamarin ya rutsa da su dai 'yan garin Ngurorre da wasu garuruwa makwabta.

Bayanai na cewa babbar motar ta rufta gada ne cikin gada a wata mummunar kwana.

Malam Muhammad Lawal, wani mazaunin garin na Ngurore ne ya kuma tabbatar wa da BBC cewa ya je wajen da abin ya faru, inda ya ga mafi yawan wadanda suka mutun matasa ne.

Ga dai karin bayanin da ya yi wa BBC:

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Hira da wani ganau kan hatsarin mota a Adamawa

To sai dai kuma hukumomi sun ce zuwa yanzu sun tabbatar da mutuwar mutum 35 ne a hatsarin, yayin da wasu 23 kuma ke kwance a asibiti ana yi masu magani, kamar yadda SP Usman Abubakar, kakakin rundunar 'yansandan jihar ta Adamawa ya shaida wa BBC.

Ya ce ana zargin yin lodi fiye da ka'ida na daga cikin abin da yua jawo hatsarin, inda ya ce dole mutame su dinga lura da bin dokokin hanya.

Akasar Ghana, karshen makon bai yi dadi ba, sabo da mummunan hatsarin mota da aka samu, inda mutane goma sha bakwai suka mutu.