Karen da ya ceto rayuwar uwargijiyarsa sau 3,500

Magic the dog
Image caption Hero kenan karen Claire

An san karnuka a matsayin dabbobin da mutane suka fi mu'amala da su da kuma yadda suke iya sunsunar abu, har ila yau suna da kokarin ceto rayuwar mutane ta hanyar gano canjin da ake samu a jini ga masu ciwon suga da kuma canjin kalar fitsari ga masu cutar kansa.

Karen mai suna "Magic" yana yin tsalle, ya dora duga-dugansa a kan gwiwoyin uwargijiyarsa, sannan ya kura mata idanu.

Wannan wata al'ada ce da yake yi sau babu adadi.

Claire Pester ta yi nazarin cewa, Magic kare ne da yake taimakon lafiyarta, an kuma horar da shi yadda zai gano ko sukarin jikinta ya hau cikin minti daya.

Ta hanyar amfani da kwarewarsa wajen sunsuna abu, Magic yana iya gano wari duk kankantarsa, yanda zai ba shi damar fadakar da Claiire lokacin da ya kamata ta yi wa kanta allurar insulin.

Ba don taimakon Magic ba, sauye-sauyen da take samu na hawan sikarinta zai iya jefata cikin mummunan hadari ko mawuyacin hali a lokuta da dama.

Claire tana da ciwon suga mai zafi, amma ba kamar yadda sauran mutane suke yin sa ba, jikinta ba ya nuna wasu alamu da zata lura dasu da ke nuna cewa ciwon zai tashi.

Ta shaidawa wani shirin BBC cewa, "Na yi amfani da fasahar zamani da muke da su, amma bai ba ni ishesshen damar da zai hana tashin ciwon ba, ko ya hana shi ya yi tsanani."

"Amma Karena Magic yana iya ba ni gargadin tsawon miti 30 cewa ina bukatar daukar mataki. A cikin shekara uku da rabin da muka yi tare da shi, ya fargar da ni daga fadawa mummunan halin da zan iya rasa raina sau 3,500," in ji ta.

"Na san ba don shi ba, da ban kawo yau a raye ba." Ta kara da cewa.

Claire tana aiki a matsayin mai kula da kananan yaran da suke da ciwon suga, tana aimakawa da kuma wayar da kai ga yara da kuma iyalansu akan ciwon suga.

Ta ce ba za ta samu damar gudanar da wannan aiki, ba tare da taimakon karenta ba, kuma za ta iya fadawa hadari.

Har ila yau samun Magic a tare da ita yana taimaka mata wajen kula da yaran da take yiwa aiki, ta kara da cewa, "Za ka iya ci gaba da rayuwarka ko kana da ciwon suga."

'Matukar gajiya'

A duka dare Magic yana bacci ne a gadon Claire.

Idan ya gano sauyi a suganta ya hau, ya kan yi amfani da duga-dugansa ya tasheta.

Image caption Magic kan tashe ta daga bacci idan ya lura ciwonta na dab da tashi

Ta bayyana cewa, "Kafin na samu wannan kare, ina tashi duk bayan sa'a daya domin na duba hawan sugan, domin na yi kokarin gano lokacin da ciwon zai iya tashi."

Wannan shi yake nuna cewa na gaji sosai. Lokuta da dama ina matukar jin tsoron na kwanta acci don gudun kar ciwon ya tashi kuma ba mai tashina.

"Yanzu na san mijina ba shi da damuwar idan ya tashi da safe wata ran zai ganni a mace a kusa da shi."

'Bincike'

Yanzu haka Hukumar kula da lafiya ta Ingila wato NHS na ci gaba da binciken gano idan za a iya amfani da karnuka wajen gano masu fama da ciwon kansa.

Binciken da aka gudanar ya bayar da damar gano cutar tun da wur-wuri, don rage masu hatsarin kamuwa da ita.

Yawancin karnukan irin su Labradors da Springer spaniels, an koya musu yadda za su gano masu fama da cutar kansa ta mafitsara daga yanayin fitsarin marasa lafiyar.

Image caption An fara amfani da karnuka wajen gano cutar kansa

Ana ganin cewa karnukan za su iya sansano warin kwayar cutar daji wanda suke fitowa daga bangaren jikin da ya kamu da cutar, suke shiga fitsarin mutum, yayin da yake kokarin fitar da kwayoyin.

Idan aka samu nasarar ganowa a cikin wadanda akai wa gwajin, za a karfafa ba su kulawa a matsayin masu cutar.

Ana rubuta ayyukan karnukan, kuma an samu wadanda suka samu nasarar kashi 90 cikin 100 na gano masu barazanar ciwon kansa.

Dr Claire Guest, co-founder of the charity Medical Detection Dogs, realised she had breast cancer after her dog, Daisy, began nudging an area of her chest which felt bruised.

Dokta Claire Guest, daya daga cikin wadanda suka kirkiri kungiyar ba da agaji ta Medical Detection Dogs, ta gano cewa tana da kansar mama bayan da karenta (Daisy) ya fara taba mata bangaren kirjinta da ya kamu.

Daga baya ta yi gwaji, sakamakon ya nuna tana da cutar.

Ceto rayuwarta da karen ya yi ne ya ja ra'ayinta wajen yadda karnuka suke gano abubuwa.

Ta bayyana cewa " kodayake karen yana da yalwar gashi da doguwar wutsiya, a gaskiya yana da nagartacciyar hanyar tantace gwaji.

Labarai masu alaka

Karin bayani