Yadda yakin Syria ya sauya rayuwar yara

Saja Hakkin mallakar hoto UNICEF
Image caption Saja ta ce tana fatan ta zama kwararriyar mai koyar da wasanni

Wannan ita ce Saja, kuma tana da shekara bakwai a lokacin da aka fara yaki a Syria a shekarar 2011. A yanzu tana da shekaru 13, ta yi fama da fadi tashi a yakin Syria kusan tsawon rabin rayuwarta.

Saja ta sauya muhalli sau biyar saboda yakin Syria.

Shekara uku bayan an fara rikicin, kaninta da aminanta hudu suka mutu a wani harin bam a Aleppo sannan ita ma ta rasa kafarta.

Kafin ta ji raunin, Saja na matukar son wasannin tsalle-tsalle. Amma a yanzu, ta ce, wasannin suna yi mata wahala kwarai saboda kafa guda gareta. Sai dai duk da haka tana fata ta cimma burinta na zama kwararriyar shugabar 'yar wasanni kuma tana fata ta yi aiki da kungiyar Olympics.

Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF, ya ce yaran Syrian sun shiga cikin kunci a shekarar 2016, inda aka kashe yara da dama fiye da adadin da aka kashe a wata shekarar yakin basasar.

A kalla yara 652 ne suka mutu kuma 255 daga cikinsu sun mutu ne a makaranta ko kusa da ita a shekarar da ta gabata.

Hakan ya sa an samu karuwar mutuwa da kashi 20 cikin 100 idan aka kwatanta da yawan yaran da aka kashe a shekarar 2015 a cewar hukumar.

Alkaluman sun hada da wadanda aka tantance ne a hukumance, inda hakan ke nufin adadin zai iya fin haka.

UNICEF, ya yi amanna cewar an dauki yara sama da 850 aikin yaki a shekarar 2016.

Rahoton ya ce alkaluman sun ninka na shekarar 2015. Akasarin wandanda aka dauka aikin suna fafatawa a bakin daga, a wasu lokutan kuma ana amfani da su a matsayin masu yin kisa ko 'yan kunar bakin wake ko kuma masu tsaron gidan yari.

Daraktan lardin gabas ta tsakiya da arewacin Afirka na UNICEF, Geert Cappelaere, ya ce ba a taba fuskantar "wahala mai tsanani kamar haka ba," a lokacin da ya ke jawabi a garin Homs da ke Syria.

Ya kara da cewa, "A kullum ana kai wa miliyoyin yara hari a Syria, an hargitsa musu rayuwarsu."

A shekara shida da suka gabata ne dai aka yi zanga-zangar kyamar Bashir al-Assad na farko a Syria. Zangar-zangar dai ta jawo rikici daga bisani kuma aka fara yakin basasa.

An gundanar da zanga-zangar farko saboda bukatar a sako wasu dalibai matasa wadanda aka tsare su kuma aka ci zarafinsu saboda sun rubuta kalaman kin jinin gwamnati.

Tun daga wancan lokacin, harin da ake kai wa kan yara yake ci gaba da karuwa a cewar asusun.

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Miliyoyin yara suna dogaro da ayyukan agaji

Mista Cappelaere ya kara da cewa, "Ko wane yaro na cikin halin dar-dar saboda halin da suke ciki sakamakon mummunan tasirin da lamarin zai iya yi kan lafiyarsu da makomarsu.

A makon da ya gabata, kungiyar agaji ta Save the Children, ta yi gargadin cewa miliyoyin yaran Syria za su iya kasancewa cikin wahala, wanda kungiyar ta ce ba za a iya sauyawa ba idan har ba a dauki matakin gaggawa ba.

Kungiyar ta kuma gano cewar kashi biyu cikin uku na yaran, sun rasa ko dai iyayensu ko an saka bam a gidajensu ko kuma sun jikkata sakamakon yakin.

Kamar yadda yaran na Syria da dama ke fatan cimma burinsu, Saja na fatan zama kwararriyar shugabar 'yar wasanni kuma tana fatan ta yi aiki da kungiyar Olympics.

Labarai masu alaka