An daga mutum-mutumin Fir'auna a Masar

Wani bangare na mutum-mutumin Hakkin mallakar hoto Empics
Image caption An gano mutum-mutumin ne a wani wurin da ake tara shara a tsakanin wasu gidaje da ke Heliopoli.

An daga wani katon mutum-mutumi na Fir'auna, wanda ake kyautata zaton ya yi shekara 3,000 daga karkashin kasa a Masar.

A makon da ya gabata ne dai aka dago wani katon kai da wasu sassan mutum-mutumin daga inda aka dago na Fir'aunan.

An gano shi ne a arewa maso gabashin birnin Alkahira a kusa da wurin bautar Ramses II, kuma masana sun yi amannar zai iya wakiltarsa.

An yi amfani da dutsen quarzite ne wajen sassaka mutum-mutumin.

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Ma'aikatar kayan tarihi ta ce za ta kai kuma ta hada bangarorin mutum-mutumin gidan adana kayan tarihi da ke tsakiyar birnin Alkahira
Hakkin mallakar hoto EPA

Ma'aikatar kayan tarihi ta ce za ta kai kuma ta hada bangarorin mutum-mutumin gidan adana kayan tarihi da ke tsakiyar birnin Alkahira, babban birnin kasar. Ta na fatan za a iya hade manyan bangarorin wuri guda.

Mazauna yankin, wadanda ke kusa da inda aka dago mutum-mutumin sun yi ta raha, daya daga cikin wadanda suka gano mutum-mutumin ya ce idan dai har ya kasance na ainihi ne, ba wai wanda aka sassaka ba, zai zamanto abu mai muhimmanci.

A makon da ya gabata ne dai kungiyar binciken ma'adinan tarihi ta gano mutum-mutumin mai nauyin ton 3, ana sa ran za a gama dago shi a wannan makon.

Labarai masu alaka