Masar ta bada damar a saki Hosni Mubarak

Tsohon shugaban Masar, Hosni Mubarak Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Nan da kwana biyu zai koma gidansa da ke birnin Alkhahira.

Masu shigar da kara na gwamnatin Masar sun bada damar a saki tsohon shugaban kasar Hosni Mubarak da ake tsare da shi a sabitin sojoji da ke birnin Alkhahira.

Matakin ba shi damar komawa gida ya biyo bayan, hukuncin da kotun kasar ta yanke a farkon wannan watan.

Haka kuma kotun ta bukaci a janye karar da ake wa mista Mubarak ta hannu a kisan masu zanga-zangar juyin-juya halin da ya hambarar da gwamnatinsa a shekarar 2011.

Kafar yada labaran Masar ta ambato lauyan mista Mubarak na cewa nan da kwanaki biyu zai koma gidansa da ke birnin Alkhahira.

A lokacin da ake tsare da shi, mista Mubarak ya yi zaman kaso na shekara 3 saboda samun shi da laifin almubazzaranci da dukiyar kasa.

Labarai masu alaka