Kotu ta daure Hamma Amadou shekara 1 a gidan yari

Hamma Amadou Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Hamma Amadou dai ya yi takarar shugabancin kasar a bara.

A Jamhuriyar Niger kotun daukaka kara ta yanke wa madugun 'yan adawa Hamma Amadou hukuncin daurin shekara daya a gidan yari bisa safarar jarirai.

An dai yanke hukuncin ne duk da cewa wanda ake zargin da kuma lauyansa ba su halarci zaman kotun ba a birnin Yamai ranar Talata.

An tuhumi tsohon shugaban majalisar dokokin da sayen jarirai sabbin haihuwa daga Nigeria shi da matarsa da kuma wasu mutanen 20.

Hamma Amadou dai ya sha musanta zargin yana cewa kutunguilar siyasa ce kawai; kuma daya daga cikin lauyoyinsa na cewa za su daukaka kara.