FA Cup: Chelsea ta yi waje da Man Utd

Premier Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Chelsea ta koma mataki na hudu a kan teburin Premier

Kulob din Chelsea ya kori Manchester United daga gasar Hukumar Kwallon Kafar Ingila wato FA Cup, bayan jefa wa Man U kwallo daya tilo, a wasan dab da kusa da karshe, da suka yi da yammacin Litinin.

Dan wasan Chelsea, N'Golo Kante ne dai ya zura wa Manchester United wanda ita ce mai rike da kofi, kwallo daya mai ban haushin.

Kuma wannan ce kwallon dan wasan ta biyu a wannan kakar wasannin, a inda dukkan su ya jefa ragar Man United din ne.

Ana dai ganin jan katin da dan wasan Man United, Ander Herrera ya samu sakamakon keta har karo biyu da ya yi wa dan wasan Chelsea, Eden Hazard ne ya ba wa Chelsea damar samun nasara.

Manchester United dai ta samu damar cin kwallo guda daya ta hannun Marcus Rashford amma golan Chelsea, Thibaut Courtois ya tare ta.

Kulob din dai ya taka wasan na ranar Litinin ba tare da fitattun 'yan wasan gaba ba da suka hada da Zlatan Ibrahimovic da Wayne Rooney da kuma Anthony Martial.

Yanzu haka Chelsea ta shiga jerin kungiyoyi hudun da za su taka wasannin kusa da na karshe da suka hada da Arsenal da Tottenham da kuma Manchester City.