Trump zai yi sadaka da albashinsa na shekara daya

Trump Hakkin mallakar hoto APTN
Image caption Mista Trump hamshakin mai arziki ne tun kafin ya hau mulkin Amurka

Mai magana da yawun fadar gwamnatin Amurka ya ce shugaban kasar Donald Trump, zai bayar da gudunmuwar albashinsa na shekara guda da ya kai dala 400,000 sadaka a karshen shekarar nan.

Sean Spicer ya ce Mista Trump ya bukaci 'yan jaridun fadar wadanda ya sha sukarsu, a kan su taimaka masa wajen zabar wadanda suka fi bukatar wannan taimako.

Ya ce, "Shugaban kasa ya bukace ku da ku taimaka masa wajen lalubo inda ya kamata wannan kudi ya isa. Kuma wannan ce hanyar da zamu bi wajen kaucewa sa idon da ake yi, shi ya sa za mu yi amfani da 'yan jarida."

A yayin yakin neman zabensa dai an yi ta rade-radin cewa ba ya bayar da sadaka yadda ya kamata, sai dai ya tsakuri kadan daga cikin abin da ya ke dashi ya bayar.

Sai dai a lokacin yakin neman zaben, Mista Trump ya ce ba shi da niyyar karbar ko sisi a albashinsa.

Amma a dokar Amurka, ba a yarda shugaban kasa ya sadakar da baki dayan albashinsa ba, dole sai ya rage ko da dala daya ce da zai amfana da ita.

Hakan na nufin a yanzu Mista Trump zai tsira ne kawai da dala dayar daga cikin albashin nasa.

Mista Trump ya zamo shugaban Amurka na uku da ya taba yin irin wannan abu na sadakar da albashinsa.

A baya, tsoffin shugabannin kasar Herbert Hoover da John F. Kennedy, su ma sun taba sadakar da albashinsu don tallafawa ayyukan agaji.

Labarai masu alaka