Me ya sa 'yan matan Canada ke kashe kansu?

Zanga-zangar da dalibai suka yi a makarantar Woodstock Hakkin mallakar hoto Mackenzie Gall/Facebook
Image caption Dalibai sun yi zanga-zangar kyamar annobar kisan kai a garin Woodstock a Ontario a shekarar 2016

Yawan 'yan matan de ke kashe kansu na karuwa a Canada. Shin ko dai jinsin mata ne ke da matsala, idan aka duba batun lafiyar kwakwalwa?

A farkon shekarar 2016 ne matasa biyar daga yankin Woodstock da ke garin Ontario, suka kashe kansu kamar dai yadda ake samun aukuwar irin lamarin a watannin da suka wuce, inda suke barin danginsu da alummarsu cikin alhini.

"Kowa yana jiran tsammani. A zaman da muka yi a wurin na lokaci kadan, ina ga kawai duk mun zauna ne muna tunanin yaushe ne za a kawo karshen wannan lamarin," a cewar Jenilee Ookcay, wata ma'aikaciyar lafiya.

Yadda 'yan mata ke kashe kansu na karuwa a sassan kasar daban-daban, yayin da kisan kai a cikin maza ke raguwa a cewar wasu alkaluma da hukumar kididdigar Canada ta fitar a ranar Alhamis.

Tun da dadewa kwararru a harkar lafiya suka bayyana damuwarsu a kan adadin kisan kai a cikin maza matasa. An kira lamarin "annoba" saboda wasu kwararan dalilai. Alkalumman sun nuna cewa, a shekarar 2013, akwai yiwuwar yawan mazan da su kashe kansu ya ninka na mata sau uku.

Amma yayin da ake zaton cewa maza za su fi kashe kansu a Canada, 'yan mata sun kusa kamo mazan a wannan lamarin. A cikin shekara goma da ta gabata, kisan kan 'yan mata ya karu da kashi 38 cikin 100, yayin da na maza ya ragu da kashi 34 cikin 100.

Karin da aka samu ya daidaita gibin da ke tsakanin jinsin biyu, inda mata suka shafe kusan kashi 42 cikin 100 na dukkan mace-macen da aka yi sanadiyar kisan kan na kasa da 20 a shekarar 2013.

Akwai makamacin wannan lamarin a Amurka, kuma a shekarar 2014, kisan kai ya zarta mutuwar mata masu juna biyu a matsayin abin da ya fi haddasa mutuwar 'yan matan da ke da shekara tsakanin 15-19 a kasashe masu tasowa, a cewar hukumar lafiya ta duniya.

Wani rahoto da hukumar da ke kula da lafiya a Canada ta bukaci masu bincike su gudunar, a kan abin da yasa aka samu raguwar kisan kan maza matasa tun cikin shekarun 1980, amma aka samu akasin hakan a 'yan mata.

Hakkin mallakar hoto John Rieti/CBC News
Image caption Wasu 'yan wani yankin a garin Woodstock sun hade kai bayan wasu jerin kisan kai da aka yi a shekarar 2016

A yayin da gwamnati za ta ware wasu kudade domin kula da lafiyar kwakwalwa a kasafin kudinta na bana da za a yi a tsakiyar watan Maris, kwararru na tunanin ko akwai bukatar gwamantin Canada ta sake tunani a kan matsayin jinsi a wurin kare kisan kai.

Masu bincike a Canada ba su san dalilin da ya sa kisan kai a wajen 'yan mata ke karuwa ba. Wasu na cewa zai iya yiwuwa saboda mata na amfani da hanyoyin da suka fi hadari ne. Wasu kuma na cewa ta yiwu saboda jami'an tsaro sun fi bayyana rahotannin kisan kan da mata ke yi.

A Canada, yunkurin da mata suke yi na kashe kansu ya ninka wanda maza suke yi sau hudu. Wasni nazari da aka yi ya nuna cewa akwai dangantaka mai karfi tsakanin tarihin cin zarafi da kuma yunkurin kisan kan.

Amma duk da haka ba kasafai ake tattaunawa a kan batun ba a duk sanda ake tattauanawa kan kisan kai da matasa ke yi, a cewar Ms Oocky, wacce ke aiki a hukumar hana kisan kai da ke Woodstock.

Ms Oacky ta ce, "idan muka bai wa al'ummarmu horo, idan aka samu wasu sauye-sauye, muna so mu sani."

Arielle Sheftall, wani mai bincike a cibiyar kare kisan kai da bincike a asibitin yara da ke Amurka, ya ce, ana bukatar karin bincike a kan irin rawar da jinsi da kuma shekaru ke takawa wajen karuwar da ake ci gaba da samu a kisan kai.

Labarai masu alaka

Karin bayani