Somalia: 'Yan fashin teku sun kwace jirgi

Jirgin ruwa Hakkin mallakar hoto MOHAMED DEEQ - SBC
Image caption Jirgin wanda aka mannawa tutuar kasar Sri Lanka ya nufi Mogadishu ne

Masu fashin teku sun kwace wani jirgin dakon mai a gabar tekun Somaliya a karon farko cikin shekara biyar.

A yammacin ranar Litinin ne jirgin ruwan ya haska fitilar da ke nuna ya na cikin matsala, inda aka ce jiragen ruwa masu gudu sun nufo shi.

'Yan bindigan da suka yi satan sun shaida wa jami'an garin cewa masunta ne su wadanda jirigin da ake kamun kifi da su ba bisa ka'ida ba ya lalata musu kayyakin aiki.

Jirgin dai ya taso ne daga kasar Djibouti zuwa birnin Mogadishu, daga nan ne masu satar a teku suka karkatar da akalar shi zuwa gabar tekun Puntland.

A baya dai an sha fama da fashin ne a kusa da tekun Somaliyan har sai lokacin da sojojin ruwa na turai suka kara yawan sintirin da suke yi har aka shawo kan matsalar.

'Yan fashin tekun dai sun kashe na'urar da za a iya gane inda jirgin ya nufa.

Kwamishinan yankin, Ali Shire Mahmud Osman, dake garin Alula a kusa da inda aka sace jirigin ya shaida wa BBC cewa ya yi kokarin gano ko masunta ne ko kuma 'yan fashin teku ne.

Ali Shire yace "bayanan da na samu sun tabbatar da jirgin dakon kaya ne dauke da Mai, sai dai ba mu san takamaimai na wacce kasa ne ba, amma muna zaton na Hadaddiyar Daular Larabawa ne, mutanen da suka sace shi sun yi ikirarin cewar masunta ne da masu su ba bisa ka ida ba sun dame su a yankin. Idan muka tabbatar barayin teku ne za mu fatattake su sannan mu ceto jirgin".

Jirgin dai na dauke ne da mai kuma mallakin Dadaddiyar Daular Larabawa ne duk da rahotanni masu cin karo da juna a kan tutar da jirgin ke amfani da shi.

Hakkin mallakar hoto MOHAMED DEEQ - SBC
Image caption Tun shekarar 2008 sojojin ruwa na kungiyar tarayyar turai ke ta aiki kusa da tekun somaliya domin dakile fashin teku.

Dakarun sojin ruwa ta Tarayyar Turai, wadda ke ayyuka domin hana fashin teku a yankin sun ce ba za a iya tabbatar da hannu masu fashi a teku da wurwuri ba.

Sojin ruwan Tarayyar Turan ta tura jirgin sama domin ya yi binciken yankin.

Anyi amannar mutum takwas ne a cikin jirgin ruwan wanda zai iya daukar a kalla ton 12,000 na kaya.

A lokacin da fashin teku ya yi kamari a shekarar 2011, an yi kiyasin ana asarar dala biliyan 8 a duk shekara.

Labarai masu alaka