Nigeria: 'A biya diyyar mutanen da aka kashe a Ile Ife'

Ibrahim Idris
Image caption Sifeto Janar na Najeriya ya aike da masu bincike kan rikicin na Ile Ife

Majalisar wakilan Najeriya ta ce daya daga cikin abubuwan da ta amince da su, kan rikicin da ya afku a Ile Ife makon da ya gabata, shi ne neman jihar Osun ta biya diyyar mutanen da suka mutu da dukiyoyin da aka yi asara.

Majalisar ta kuma cimma matsayar yin bincike kan hakikanin abin da ya faru bayan wata muhawara kan rikicin, a zamanta na ranar Talata.

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da rahotanni ke cewa an kama wasu jami'an tsaro da ake zargi da hannu wajen kisan mutanen da suka mutu.

An samu naira miliyan 49 jibge a filin jirgin sama na Kaduna

Sai dai kuma wani abu da har yanzu ba a iya tantancewa ba dangane da rikicin na Ile Ife, shi ne hakikanin adadin mutanen da suka mutu.

Ga dai karin bayanin da Dr. Abdullahi Balarabe Salame, dan majalisar wakilan Najeriya daga jihar Sakkwato ya yi wa Haruna Shehu Tangaza, kan batun.

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Dr. Abdullahi Balarabe Salame