'Yan mata hudu sun kai hari a Maiduguri — NEMA

Wata mota na cin wuta
Image caption Kungiyar Boko Haram ta dauki alhakin wasu hare-haren kunar bakin waken da aka yi a baya a Maiduguri

Kimanin mutane shida ne suka rasa rayukansu ciki har da 'yan kunar bakin wake mata hudu, a wani harin da suka kai a wajen garin Maduguri a daren ranar Talata.

Jami'in hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa, yankin arewa-maso gabas, Muhammad Kanar wanda ya tabbatar wa da BBC aukuwar lamarin, ya ce wasu mutane 16 kuma sun samu raunuka a sanadiyyar harin.

Inda ya kara da cewa, "An kawo su ne a mota su hudu kuma duk yara mata ne, inda aka sauke su a unguwar Usumanti da ke kan titin Muna a wajen birnin Maiduguri."

"Kuma a nan ne suka tayar da bama-baman da ke jikinsu," in ji jami'in.

Wadanda suka jikkatan dai na ci gaba da karbar magani a asibiti.

Birnin na Maiduguri wanda a da nan ne tungar 'yan kungiyar Boko Haram, ya sha fuskantar harin kunar bakin wake daga 'yan kungiyar.

Kungiyar dai na yin amfani da mata sosai wajen kai hare-haren kunar-bakin-wake, inda a kwanakin baya suka fito da salon yin amfani da mata dauke da jarirai domin bad-da-sawu.

Hakan na faruwa bayan rundunar sojin kasar ta ce ta ci karfin su, lamarin da ya sa suka rasa mafada.

Kiyasi ya nuna cewa rikicin kungiyar ta Boko Haram ya yi sanadin mutuwar sama da mutum 20,000 sanna ya tilasta wa fiye da mutum 2.6m barin gidajensu.

Labarai masu alaka