Abin sauraron sauti ya kona wata mata a jirgi

Fuskar wata mata Hakkin mallakar hoto Australian Transport Safety Bureau
Image caption Matar ta kone a hannunta kuma hayakin wuta ya bata mata fuska

Hukumomi a Australiya sun yi gargadi kan hadarin da ke tattare da amfani da na'urorin da ake amfani da su wajen cajin batiri a cikin jirgi, bayan da earpiece ya din wata mata ya kama da wuta.

Matar tana tsaka da bacci ne a cikin jirgin da ya tashi daga birnin Beijin na China, zuwa birnin Melbourne na Australiya, sai karar fashewar wani abin ta farkar da ita.

Ta yaga ear piece din inda ta ga yana fitar da tartsatsin wuta, sai kuma na'urar ta kama da wuta har ta fara narkewa.

Fashewar earpiece da kuma wutar da ta kama ta shafi fuskarta inda ta yi bakikkirin, ta kuma bar mata tabon kuna a hannayenta.

"Da farko na kawar da fuskata, wadda ta janyo ear piece din ya nannade min wuya. Na ci gaba da jin zafin wuta sai na yi gaggawar yakice na'urar na wurgar da ita a kasa. Yana ta tartsatsi tare da fitar da wuta kadan-kadan.

Hakkin mallakar hoto Australian Transport Safety Bureau

Ma'aikatan cikin jirgin sun yi gaggawar kawo taimako, inda a karshe suka yi nasarar kashe wutar ta hanyar sheka bokiti guda na ruwa a kan na'urar sauraron sautin.

Zuwa wannan lokaci batirin da kuma murfin robar sun narke a kasa.

A rahoton da ta fitar, Hukumar ATSB din ta ce, "Daga bisani an bar sauran fasinjojin jirgin da shakar warin konanniyar roba da sauran kayan lantarki da kuma na konannen gashi."

Rahoton bai ambaci ko ear piece din mallakin ko wanne kamfani ne ba, amma an yi amannar cewa na'urar cajin batirin waya ne ya jawo faruwar lamarin.

Hakkin mallakar hoto Reuters

Tuni dai hukumar ATSB ta wallafa shawarwari a kan yadda za a dinga amfani da batiran cajin waya a cikin jirgi, tana mai gargadi cewa, "Kamar yadda ake samun karuwar amfani da batiran cajin waya, to haka ma ake samun karuwar barazanar jawo wani lamari wajen yin amfani da su lokacin yin bulaguro a jirage."

A 'yan shekarun nan ana yawan samun matsalolin da suka danganci batiran cajin waya a jirgi.

A bara ma sai da aka dakatar da wani jirgin da ya tashi daga birnin Sydney, lokacin da aka ga hayaki ya fara fitowa daga cikin kayan matafiya da suke shiga cikin jirgi da su. Da aka bincika sai aka ga ashe batirin cajin waya ne ya kama da wuta a cikin kayan.

Karin bayani