Yadda rayuwa cikin tsaunuka take a kasar Cape Verde?

Martin Plaut ya gano cewa : Dutse mai aman wuta mai karko na tsibirin Kasar Cape Verde, ya sa gabar tekun Afrika ta yamma, ta fi sauran rairayin bakin teku daraja, wanda 'yan yawon bude ido suke morewa kallo. Ko wane tsibiri yana da yanayinsa na musamman.

Hakkin mallakar hoto Martin Plaut
Image caption Kasar Cape Verde na da sarari mai fadi na musamman wanda dogayen tsaunuka da kwari masu zurfi suka mamayeta. A sakamakon haka, filin noma ke matuakar wahala.
Hakkin mallakar hoto Martin Plaut
Image caption Yawancin duwatsun da suke fitar da ruwa kamar na kasar Sao Vicente dadaddu ne, amma a kusa da tsibirin kasar Fogo, an samu dutsen da ya fara aman wuta a shekarar 2014, wanda ya tilastawa daruruwan mutane barin gidajensu. Sakamakon haka ne mutane da yawa 'yan asalin kasar Cape Verde din suka tsalla wasu kasashen.
Hakkin mallakar hoto Martin Plaut
Image caption Yayin da ake wahalar samun kasar noma, kasar dutse mai aman wutar na samar da yalwar kayan marmari da ganyayyaki don siyarwa a kasuwanni. Duk da haka suna da karancin ruwan sama, kuma dole ne a yi taka-tsan-tsan wajen yin amfani da ruwa don tabbatar da an samu na noma.
Hakkin mallakar hoto Martin Plaut
Image caption Mazauna gurin da ba sa kamun kifi ko noma na dauko abincin dabbobi su gangaro ta kan tsibirin.
Hakkin mallakar hoto Martin Plaut
Image caption Tun lokacin da suka samu 'yancin kai a shekarar 1975, gwamnati ta zuba hannun jari mai yawa a bangaren ilimi don inganta rayuwar 'yan kasar. A yanzu, suna da makarantu har a cikin kauyuka, wanda hakan ya sa kashi 70 cikin 100 na 'yan kasar masu ilimi ne.
Hakkin mallakar hoto Martin Plaut
Image caption Kamar yadda kasar ta dauki zuwa makaranta da muhimmanci, haka kasar ta dauki aikin soji da muhimmanci inda ake sa matasa daga shekara 18. Kasar tana alfahari da rawar da ta taka tare da kasar Guinea Bissau a fafutukar neman 'yancin kai daga Turawan mulkin mallaka Portugal.
Image caption Tarihi kasar ya fi gaban fafutukar neman 'yancin kai - wannan adon da aka yi wa garin Mindelo na tunawa ne da lokutan da Cape Verde ke samar da tashar makamshi ga sojin ruwan Birtaniya.
Hakkin mallakar hoto Martin Plaut
Image caption 'Yan kasar Cape Verde na shan fama wajen samun rufin asiri, sai dai ana samun hasken rana da yanayi mai dadi ko yaushe a kasar, wanda hakan ya sa tsibirin na su ya zama tamkar aljannar duniya ga masu yawon bude ido, inda suke zuwa walawa.

Daukar hoto by Martin Plaut

Karin bayani