An ceto mutum 5,000 daga BH a tsaunukan Mandara

Boko Haram Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Boko Haram sun koma kai hare-haren kunar bakin wake tun bayan da dakarun Najeriya suka koresu daga dajin Sambisa

Rahotanni daga jamhuriyyar Kamaru na cewa an ceto fiye da mutum 5,000 daga hannun 'yan Boko Haram tun watan a Janairun 2017.

Ministan yada labarai na Jamhuriyar Kamaru Issa Tchiroma Bakary, ya ce, fiye da mutum 5,000 ciki har da yara da mata aka 'yanto daga mayakan kungiyar Boko Haram, inda aka kashe 60 daga cikin mayakan tun a karshen watan Janairu.

Mista Bakary wanda shi ne mai magana da yawun gwamnatin kasar, ya kara da cewa dubban sojin kasar tare da tallafin sojin Najeriya ne suke kaddamar da hare-hare kan sansanonin 'yan Boko Haram a tsaunukan Mandara, wadanda suka ratsa kasashen biyu tun ranar 26 ga watan Janairu.

"A kalla an kashe yan ta'adda 60 kuma an kama mutum 21, wadanda a yanzu haka suke taimaka wa jami'an tsaron Najeriya da na Kamaru da bayanai a binciken da suke yi," in ji Bakary.

Ya ce, "An lalata wata mafakar masu tayar da kayar bayan a tsaunukan Mandara kuma an lalata wurin ajiyar man fetur da kuma wurin kera ababen fashewa."

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Sojin Najeriya da na Kamaru sun fara kaddamar da hare-hare kan tsaunukan Mandara ne ranar 26 ga watan Janairun bana

Mista Bakary ya kuma ce sojoji sun lalata gidan wani shugaban Boko Haram inda kuma can ne mafakar mayakan, an kuma lalata makamai da motoci da babura da ke gidan.

Ya ce ba a kashe soja ko daya ba.

An kai mutanen da aka 'yanta din, wadanda suka hada da tsoffi, wani sansanin 'yan gudun hijira da ke garin Banki a Najeriya, inda suke samun kulawa daga ma'aikatan kiwon lafiya na sojin Najeriya da Kamaru.

A watan Disambar da ya gabata ne, shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya bayar da sanarwar cewar sojoji sun kori 'yan Boko Haram daga muhimman wuraren da suke fakewa, wadanda suka saura a dajin Sambisa, wani tsohon sansanin 'yan Boko Haram din da ya ratsa cikin kasashen biyu.

A wannan watan ne Najeriya da Kamaru suka bude hanyar da ke kan iyakar kasashen biyu a karon farko cikin shekara uku.

Tuni Kamaru ta yi kira ga mutanen kasar da sojinta da su sa ido su kuma hada kai, ganin yadda masu tayar da kayar bayan suka koma yin amfani da kai harin kunar bakin wake a lokacin da karfinsu ya ragu.

Rikicin kungiyar Boko Haram da aka shafe shekara bakwai ana yi, ya kashe fiye da mutum 20,000 kuma ya raba mutum miliyan 2.6 da gidajensu, inda mutum miliyan biyar ke bukatar agajin abinci na gaggawa.

Labarai masu alaka