Majalisa za ta tilastawa shugaban Kwastam amsa kiranta

Hameed Ali Hakkin mallakar hoto .
Image caption Shugaban Kwastam, Hameed Ali, ya kasa bayyana a gaban Majalisar Dattawan Najeriyar

A ranar Alhamis ce Majalisar Dokokin Najeriya ta yanke shawarar tilastawa shugaban hukumar hana fasa kaurin kasar, Hameed Ali, bayyana a gabanta.

Rahotanni sun ce Majalisar ta cimma matsayar ne bayan wani kuduri da Sanata George Sekibo ya gabatar, na neman majalisar ta yi amfani da damar da sashe na 89 na kundin tsarin mulkin kasar ya bayar, domin tilasta wa Hammed Ali ya bayyana a gaban majalisar.

Bayan mataimakin shugaban majalisar Ike Ewkwerenmadu ya goyi bayan kudurin ne, sai shugaban majalisar Bukola Saraki ya yanke hukuncin tilastawa Hameed Ali bayyana a gaban majalisar.

Sashi na 89 na kundin tsarin mulkin kasar ya bai wa majalisar ikon gayyatar ko wane dan Najeriya don yin bincike a kansa.

Shugaban hukumar kwastam din ya rubuta wasika ga majalisar a ranar Talata, inda ya shaida wa matasar cewar ba zai iya amsa gayyatar da aka yi masa ba, domin lokacin ya ci karo da wani zama na musamman da hukumarsa za ta yi.

Hakkin mallakar hoto NIGERIAN CUSTOMS
Image caption A kwanan nan ana takun-saka tsakanin Majalisar Dattawan Najeriya da kuma hukumar hana fasa kaurin kasar

Lamarin ya fusata 'yan majalisar, kuma bayan haka ne suka yanke hukunci cewa dole ya bayyana a gabanta ranar Laraba.

Wannan ne ya sa ya sake rubuta wasika ga majalisar inda ya roke ta ta yi hakuri domin an yi masa rasuwa ne.

Bayan an karanta wasikarsa ta biyu a zauren majalisar, 'yan majsalisa sun kara harzuka suna masu cewa ba za su yarda a ci mutuncin majalisar ba.

Amma yunkurin babban mai tsawatarwar na majalisar, Sanata Olusola Adeyeye, na neman majalisar ta sa a kama shugaban kwastam din bai yi nasara ba domin sauran takwarorinsa sun yi ta ihu suna cewa ba su goyi baya ba.