Nigeria: Zan yi a-yi-ta-ta-kare da cin hanci da rashawa -Magu

EFCC Hakkin mallakar hoto EFCC
Image caption Karo na biyu kenan da Majalisar Dattawan najeriya ke kin tabbatar da Ibrahim Magu a masatyin shugaban hukumar EFCC

Shugaban hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya ta'annati (EFCC), Ibrahim Magu, ya ce kin tabbatar da shi a mukaminsa ba zai sa shi ya daina yaki da cin hani da rashawa ba.

Magu, wanda ya yi wannan tsokacin a kofar majalisar a lokacin da yake gana wa da masu fafatukar kare hakkkin bil adama bayan an ki tabbatar da shi a mukaminsa, ya ce shi zai ci gaba da yakin ko an tabbatar da shi ko ba a tabbatar da shi ba.

Ya ce babu take hakkin bil daman da ya kai cin hanci da rashawa inda ya ce alhakin yaki da cin hanci da rashawa ya rataya ne a kan kowa.

Shugaban na EFCC ya ce shi zai 'yar a-yi-ta-ta-kare da cin hanci da rashawa.

Magu ya ce zarge-zargen da aka yi masa ba za a iya tabbatar da su ba, yana mai karawa da cewar ba a ba shi damar kare kansa ba.

Hakkin mallakar hoto EFCC
Image caption Shugaban EFCC, Ibrahim magu ya sha tambayoyi yau a zauren Majalisar Dattawan Najeriya

A yau ne dai Majalisar dattawan Najeriyar ta yi watsi da tabbatar da shugaban Hukumar EFCC, Ibrahim Magu, a mukaminsa bisa wani rahotan hukumar 'yansandan farin kayan ta kasar ta kai ma ta.

Me ya sa Buhari ya sake tura sunan Magu majalisa?

Amma wani dan Majlisar dattawan kasar, Sanata Ali Ndume, ya ce majalisar ba ta da hurumin cire Magu daga mukaminsa saboda babu dokar da ta hana shugaban Najeriyar ya ba wa mutum aiki na riko kuma babu wa'adin iya yaushe zai iya yin aiki akan hakan.

Sanata Ndume ya ce Magu ya rigaya ya kare kansa a kan dukkan zarge-zargen da aka yi masa a cikin rahoton na 'yansandan farin kayan kasar.