Wasika daga Afirka: Yadda 'yan Najeriya ke matukar kwadayin rayuwa a Amurka

Wani dan Najeriya da ya samu takardar zama dan kasa Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption 'Yan Najeriya da dama na buluguro zuwa Amurka saboda su haihu a can

Babu abinda zai hana 'yan Najeriya kwadayin Amurka, a cewar marubuciya, Adaobi Tricia Nwaubani. Ko shawarar baya bayan nan da wata mataimakiyar Shugaba Buhari ta bayar 'yan kasar masu iznin shiga Amurka da su dage tafiyarsu zuwa kasar; ga 'yan Najeriya, Amurka ita ce tundun-mun-tsira. Kuma ga 'yan Najeriya da dama Amurka aljanna duniya ce.

Tsarin inshora

A Amurka kadangaru suna rikidewa su zama kadajoji. Kana daga cikin wadanda suka yarda da wannan wautar? Kai dan bora ne? Wanda baya ji? Kar ka damu. Amurka zata sa rayuwarka ta canza. Kuma idan ka koma Najeriya hutu, 'yan kauyenku baki daya za su zo su tarbe ka daga filin jirgin sama.

Amurka tamkar inshora ce ga rayuwar yara a gaba. Ma'aurata da dama a Najeriya ba su damu su yi rance domin su tafi kasar su haihu ba kawai saboda da zarar ka haihu a can, za a bai wa yaro takardar shaida zama dan Amurka wanda zai bai wa jaririn kyakyawar rayuwa nan gaba.

Kar kuma mu manta da saye-sayen kayayyaki. Amurka tana da kyawawan misalai na amfanin tsarin jari hujja. 'Yan Najeriya wadanda suke da kudi suna bukatar inda za su kashe su.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Zuwa Amurka zama tashin hankali ga 'yan Najeriya tun lokacin da Donald Trump ya karbi mulkin kasar

To idan fa ya kasance abinda mai bai wa shugaba Buhari shawarwari ta fada dai-dai ne kuma an hana wasu 'yan Najeriya masu sahihiyar takardar iznin shiga kasar Donald Trump din.

Mun gode da wannan sanarwar taka. Ka kyauta kwarai da gaske. Abinda za mu yi kawai shi ne, za mu kara sunayen jami'an tsaron iyakar Amurka a jerin wadanda muke so mu yi nasara a kan su a yayinda muke shirin zuwa aljannar duniyar.

'Yan Najeriya da dama sun bayyana yadda jami'an da ke ganawa da masu neman iznin shiga Amurka a offishin jakadancinta ke nuna wa mutune isa irin ta 'yan mulkin mallaka a lokacin jarrabawar.

Adaobi Tricia Nwaubani:

Hakkin mallakar hoto Adaobi Tricia Nwaubani

"Yan Najeriya da dama sun bayyana yadda jami'an da ke yin gwajin samun takardar iznin zuwa Amurka a ofishin jakadancinta ke nuna wa mutune isa a lokacin jarrabawar.."

Cewa suke: " Matar ta tsare ni da idanu". Ni ma kuma sai na tsatsareta da idanu." Bata duba takarduna ba. Na cigaba da tsare ta da idanu. Ban dauke idanu na daga kanta ba. Sai ta yi da fuskarta kamar za ta hana ni takardar iznin, amma a zuciyata sai na yi addu'a na ce Allah na bar maka al'amarin nan a hannunka.

A zuciyata, kawai na san za a bani iznin. Amma kwatsam, sai ta bata rai ta ce na dawo na karbi bizata. Ba ta ma san yadda na ji ba. Allah ya karbi addu'ata ya sa ta bani".

'Asirin neman Bisa'

Amma kar ka shagala ka yi zaton da sauki. Sau tari, 'yan Najeriya masu neman bisar dalibai ko ta baki ko 'yan ci rani da dai sauransu sukan yi 'yan asirce - asirce kafin suje nema.

A bangera guda kuma, akwai mata da maza da suka kware a neman. Wasu na bayar da shawarwari kan abubuwan da zaka fada da kuma wadanda bai kamata ka fada ba wurin jarrabawar neman bisar, ta yadda mutum zai samu.

Wasu na taimaka wa da cike takardun neman takardar izinin shiga Amurka.

"Idan har wannan mutumin ya cike miki takardun amsa tambayoyin neman bisa, "mutane su kan ce" ba yadda za a yi ma su hana ka ita. Ya san abinda ya kamata mutum ya rubuta.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Akwai masu taimaka wa da cike takardun neman takardar izinin shiga Amurka.

A wasu lokutan masu neman bizar su kan dukufa wajen addu'oi da azumi ko kuma su ziyarci wani malami ko boka wanda zai yi 'yan dabaru domin su samu shiga kasar.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Wasu bokaye suna bayar da tabbacin samun bisar

"Idan har suka bi umarnin da na ba su ba za a taba kama su ba. A ranar babu wanda zai gane abinda suke tafe da shi.

Tsibbace-tsibbacen da yake yi kan iya makantar da na'urorin da ake amfani da su wajen binciken kayan matafiya.

Gaba gaba ma masu tsibbun za su rika shaida wa mutune ranar da su tafi saboda su asirce masu tsaron kan iyakar Amurka saboda su ce musu "barkanku da shigowa Amurka" ta yadda da kyar ma za su kalli bisar ta su.

Karin bayani