Majalisa ta sake watsi da sunan Magu

Buhari
Image caption Wannan ne karo na biyu da majalisar ta ki tabbatar da Ibrahim Magu

Majalisar dattijan Najeriya ta sake watsi da sunan Ibrahim Magu, na tabbatar da shi a matsayin shugaban hukumar da ke yaki da masu yi wa tattaklin arzikin kasa zagon kasa EFCC.

Wannan dai shi ne karo na biyu da hukumar ta ki amincewa da Mista Magu a matsayin shugaban EFCC din.

Shugaban majalisar dattawan Sanata Bukola Saraki ya ce, kin amincewa da tabbatar da shi da majalisar ta yi na nufi zai sauak daga shubancinta na riko da yake yi.

A don haka sanata Saraki ya umarci shugaban kasar Muhamadu Buhari da ya sake zabar wani daban da zai yi shugabancin hukumar ta EFCC.

Me ya sa Buhari ya sake tura sunan Magu majalisa?

Yadda ta kaya a majalisar

'Yan majalisar sun ki tabbatar da Mista Magu ne a matsayin shugaban hukumar EFCC bayan doguwar muhawarar tambaya da amsa da ta faru tsakanin sa da 'yan majalisar.

Daga cikin tambayoyin da suka kai masa akwai batun cewa me ya sa hukumar EFCC ba ta bin umarnin kotu, da batun da ke cewa ana take hakkin dan adam, da yadda Mista Magu zai iya yaki da cin hanci a bangaren shari'a da kuma hanyoyin da ake bi wajen tsare wadanda ake zargi.

Mista Magu ya ce, akwai wani mai kare hakkin dan adam da ya ce kurkukun EFCC tamkar otal suke, don haka ba batun cin zarafin bil adama ta wannan fuska.

An kuma yi masa tambaya a kan ko zuwa yanzu nawa hukumar ta samu damar karbowa tun bayan da ya fara shugabancinta na rikon kwarya.

Sai ya ce, ''Zai yi matukar wahala in bayar da rahoton nawa aka kwato zuwa yanzu a yakin da muke da cin hanci da rashawa."

Mista Magu ya ce duk da cewa ba lallai ne matakan da jami'an hukumar ke dauka a ko yaushe su zama daidai ba, EFCC na iya kokarinta don ganin ta yi abin da ya dace.

Kan batun kwarmatai bayanan da ake yi kan wadanda ake zargi da almundahana kuwa, Mista Magu ya ce hukumar na kokarin kara gyara fasalin tsarin.

Ya ce, ba ma zai yi mamaki ba idan masu kwarmatai bayanan suka kai jami'an tsaro gidansa, don ganin cewar yanzu yana da babban gida.

Bayan daukar dogon lokaci da 'yan majalisar suka yi suna yi wa Mista Magu tambayoyi, a karshe shugaban Majalisar Bukola Saraki, ya tambaye su ko sun amince da Magu a matsayin shugaban EFCC, inda mafi yawan su suka ki amincewa.

Daga bisani Sanata Saraki ya tabbatar da watsin da majalisar ta yi da tabbatar da Mista Magu a karo na biyu.

Amma Sanata Ali Ndume, ya mike tsaye inda ya ki amincewa da lamarin, sai dai hakan bai yi wni tasiri ba.

Labarai masu alaka