Tanzania: An kori 'yan jarida kan yi wa Trump 'ƙage'

Shugaba Donald Trump Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Labarin ya ce mista Trump ya kira Mista Magafuli a matsayin "Gwarzon Afirka"

Kafar yada labaran TBC ta kasar Tanzaniya ta kori ma'aikatanta tara bayan sun yada wani labari cewar shugaban Amurka Donald Trump, ya yabi ƙwazon shugaban kasar, John Magufuli.

Labarin dai ya bayyana ne a shafin yanar gizo na tashar talabijin din Fox.

Labarin, wanda aka wallafa a makon da ya gabata, ya ce Mista Trump ya kira Mista Magafuli a matsayin "Gwarzon Afirka" idan aka kwatanta shi da sauranu shugabannin wadanda "basa aikin komai"

A wata sanarwa da ta fitar, TBC ta ce ba a bi ka'idojin yada labarai.

Labarin ya bayyana cewa shugaban Amurka ya yi kira ga sauran shugabannin Afirka da su bi sahun Mista Magafuli, inda ya jadadda batun shugabanci na gari da kuma yaki da cin hanci da rashawa.

Mista Magafuli, wanda aka kira "Sarkin cika aiki" saboda yadda yake gudanar da shugabancinsa, na yaki da cin hanci da rashawa kuma ya samu goyon bayan 'yan kasar har ma da na kasashen waje.

Labarin ya ce Mista Trump ya yi furucin ne a yayin da yake saka hannu kan dokar da ta hana wasu 'yan Afirka shiga Amurka, "daga kasashen da shugabanninsu ba sa tabuka abin a zo a gani, da kuma na wadanda shugabannin ba sa son barin mulki."

Image caption An shaidi Mista Magafuli kan yin aiki ba sani ba sabo

Labarai masu alaka