Nigeria: 'Faduwar darajar Naira za ta shafi aikin hajjin bana'

Hukumar aikin hajjin Najeriya ta ce tana daukar matakai
Image caption Ana dai ganin aikin hajjin bana sai mai idanu da tozali

Hukumar Alhazan Najeriya ta ce tana daukar matakan ganin maniyyata aikin hajjin bana sun samu damar biyan kudin aikin.

Da alama dai biyan kudin kujerar zuwa aikin hajjin a Najeriya zai yi wa mafi yawancin maniyyatan na bana wuya, saboda yadda darajar kudin kasar ta ke a yanzu.

Wannan ne ya sa hukumar ta ce ta fara daukar wasu matakai domin ganin ta rage wa maniyyatan tsadar da take ganin kujerar Hajjin za ta yi.

Ku saurari hirar da kakakin hukumar, Alhaji Uba Mana ya yi da Haruna Shehu Tangaza kan yadda lamarin yake a halin yanzu:

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Kakakin hukumar aikin hajjin Najeriya, Uba Mana