An gano daimon mai girman gaske a Saliyo

Masu aikin hakar ma'adinai Hakkin mallakar hoto OLIVIA ACLAND
Image caption Akwai masu aikin hakar ma'adinai da dama a Saliyo

Wani malamin addinin kirista, Fasto Emmanuel Momoh ya gano wani diamon a lardin Kono wanda ya zama daya daga cikin daimon mafi girma da ake da su a duniya.

Kuma an adana diamon din mai nauyin carat 709, a babban bankin kasar da ke Freetown.

Daimon din ya zamo daya daga cikin diamon mafi girma guda 20 da aka taba hakowa a duniya.

Wakilin BBC da ke Saliyo, Umaru Fofana ya ce ba akwai dillali da masu hada-hadar ma'adanai da dama a yankunan da ke da arzikin diamon a kasar.

Sai dai ya kuma bayyana cewa babu tabbaci ko al'ummar lardin za su amfana daga diamon din da aka gano.

Daimon din da ba a kai ga sanin darajar kudinsa ba tukuna, shi ne mafi girma da aka taba hakowa a Saliyo tun a shekarar 1972, a lokacin da aka tono diamon mai maunin carat 969.

Da farko dai an kai diamon din fadar shugaban kasar, Ernest Bai Koroma a ranar Laraba kafin a kai shi babban bankin kasar inda aka adana shi.

A wata sanarwa da fadar shugaban kasar ta fitar, shugaban ya mika "godiya" ga sarki da kuma mutanensa da ba su yi fasa-kaurin diamon din daga kasar ba.

Hakkin mallakar hoto UMARU FOFANA
Image caption Nauyin diamon din ya kai 709 na ma'aunin carats

Mista Koroma ya kara da cewa kamata ya yi 'yan kasar baki daya su ci moriyarshi.

Kasar ta Saliyo ta yi fice wajen arzikin ma'adanin diamon, amma kuma suna da tarihin rashin gaskiya.

Cinikin diamon na daga cikin abin da ya janyo yakin basasar da aka shafe shekaru ana yi, a lokacin da kungiyoyin 'yan tawaye suka yi musayarsu da makamai.

Labarai masu alaka