'Yan fashin teku na barazana a Somaliya

Mai tsaron gabar teku Hakkin mallakar hoto Google
Image caption Fashin ya jawo muhawara tsakanin kamfanonin da ke sana'ar aike wa da sakonni ta jiragen ruwa

Wani fashi da aka yi a wani jirgin ruwan dakon mai a kusa da gabar tekun somaliya a makon da ya gabata ya girgiza wasu masu sana'ar aikewa da sakonni ta jiragen ruwa.

Wannan ne karo na farko da 'yan fashin teku suka yi nasarar fashin jirgin ruwa, mai dakon mai na wata kasar tun a shekarar 2012.

Fashin ya jawo muhawara ]kan ko kamfanonin da ke sana'ar aike wa da sakonni ta jiragen ruwa sun gamsu da haduran dake tattare da fashin teku.

Jirgin ruwan, samfurin MT Aris 13 na kan hanyarsa ne ta zuwa Mogadishu daga Djibouti a ranar 13 ga watan Maris, inda maimakon ya nisanta kanshi daga tekun Somaliyan, sai ya bi gajeriyar hanya dake tsakanin kuryar kusuwar Afirka da tsibirin Socotra da ke Yemen.

Masu fashin tekun Somaliyan sun far wa jirgin da wasu jiragen ruwa masu gudu sosai guda biyu, kilomita 17 bayan ya bar gabar tekun, yayinda suka rika nuna makamansu ga ma'aikatan jirgin ruwan.

Masu fashin sun sace Jirgin ruwan da ma'aikatanshi 'yan Sri Lanka kuma suna cigaba da tsare su har sai an cimma yarjejeniya kan kudin fansa ko kuma idan hukumomin lardin Puntland sun kubutar da su.

Wannan na nufin, a halin yanzu, ma'aikatan jirgin ruwa 16 ne masu fashin dake zaune a somalia ke tsare da su.

"Rashin kariya"

Hakkin mallakar hoto FRANK GARDNER/BBC
Image caption A shekarun baya bayan nan, kungiyar tarayyar turai da ma wasu kashen, sun saka sojin ruwa masu yawo

Wani mai magana da yawun hukumar tsaron teku na Neptune ya ce, " jirgin da zai bi ta gabar tekun Somaliya ba tare da masu tsaron dake dauke da makamai ba, yana nuna cewa ya amince kuma ya gamsu da yanayin tsaron tekun".

Duk da cewa a baya, masu fashin teku sun kware wajen makalewa gefen manyan jiragen ruwa a yayinda suke tafiya, yana da matukar wahala su iya yin haka idan yana gudu sosai, musaman idan matukin jirgin ya dauki muhimman matakai.

A shekarun baya bayan nan, kungiyar tarayyar turai da ma wasu kashen , wandanda suka hada da China, sun saka sojin ruwa dake tsare tekun da kuma jerin gwanon 'yan rakiya a gabar tekun Yemen domin kariya daga 'yan fashin tekun somaliya.

Za a dauki Matakai?

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption A shekarar 2010 ne fashin teku ya yi kamari a Somaliya

Shin wannan al'amarin zai sa a dauki kwararan matakai a kan teku ko kuma zai zama somawar wani sabon fashin teku?

Abin damuwar shi ne, har yanzu ana fama da dalilan da suka sa masuntan Somaliya suka koma fashin teku a shekaru goma da suka gabata.

A yanzu, somaliya na fama da matsananciyar yunwa da talauci kuma babu isassun aikin yi a kasar.

Lamarin ya yi kamari

A shekarar 2010 ne fashin teku ya yi kamari a Somaliya, a bangarorin sace-sacen jiragen ruwa da kuma ma'aikatansu da ake garkuwa da su domin karbar kudin fansa.

Bayan haka, ba da dadewa ba kamfanonin da ke san'ar aikewa da sakonni ta jirgin ruwa suka fara saka ma'aikatan tsaro masu dauke da makamai a cikin jiragensu "wadanda ke barazana ga 'yan fashin tekun da makamansu kuma a wasu lokutan su kan yi harbi domin yin gargadi gare su.

Bayan shekarar 2010, sai ya kasance ba za su iya aikata abin da suke yi ba, ba tare da an hukuntasu ba. Amma yanzu akwai yiwuwar, an yada jita-jitar cewa jiragen ruwa da dama ba su daukan makamai, wanda hakan ya tayar da hankula, domin ana ganin cewa 'yan fashin tekun somaliyan za su dawo da fashin da suka saba yi.

Labarai masu alaka