An kayar da Issa Hayatou a zaben CAF

Ahmad Ahmad, sabon shugaban Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Ahmad mai shekara 34 ya ci kuri'u 54 a zaben da aka gudanar a Habashan

An zabi Shugaban kungiyar kwallon kafar Madagasca, Ahmad, a matsayin sabon shugaban hukumar kwallo kafa ta Afirka.

A ranar Alhamis ne aka gudanar da zaben shugaban hukumar a Addis Ababa, babban birnin kasar Habasha inda Ahmad na kasar Madagascar ya doke dadadden shugaban hukumar ta CAF Isa Hayatou na kasar Kamaru.

Ahmad ya ci zaben da kuri'a 34 daga cikin 54 da aka kada.

Sakamakon zaben na nufin sauyi a shugabancin hukumar a karon farko tun lokacin da Hayatou na Kamarou ya karbi mulkin a shekarar 1988.

Ahmad dai zai kasance shugaban hukumar na bakwai a shekaru 60 a tarihin CAF.

Tafiyar Hayatou wata gagarimar sauyi ce ga kwallon kafan Afirka kuma dan shekara 70 din zai rasa matsayinsa a hukumar kwallon kafa na duniya, Fifa da na gudanarwarta.

Sau biyu yana karawa da wasu 'yan takarar a zaben shugabancin hukumar kuma a duka lokutan biyu ya yi gagarumar nasara.

A wannan karon kuri'u 20 kawai ya samu, wanda ya kawo karshen fatan da yake yi na yin nasara a karo na 18 a kan matsayin, wanda zai bashi daman shugabancin hukumar a cikin shekara 29..

Labarai masu alaka