Trump zai yi amfani da kudin tallafi domin karfafa tsaron Amurka

TRUMP
Bayanan hoto,

Shugaba Trump ya sha alwashin alkawarin sa Amurka gaba da kowa a lokacin yakin neman zabensa

Gwamnatin shugaba Trump ta fitar da shirye-shiryen bunkasa kundin da take kashewa kan harkar tsaron Amurka da dala biliyan 54 a dai-dai lokacin da ta rage kudin tallafi a kasashen waje.

Za a mika kasafin kudin gwamnatin tarayyar Amurkar ga Majalisar Dokokin kasar.

Ma'aikatar harkokin wajen Amurka na fuskantar ragi a kasafin kudinta na kashi 28 cikin 100.

Har ila yau hukumar kiyaye muhallin kasar na dab da rasa wani kaso cikin kasafin kudinta musamman kan batutuwan da shugaba Trump bai yarda da su ba, irinsu sauyin yanayi da kuma makamashin da ba ya karewa.

Batutuwan sun hada da shirye-shiryen dai-daita sahun Amurka bisa hakkokin da suka rataya a kanta a yarjejeniyar yanayi na Paris.

Jaridar New York Times ta ruwaito cewar za a iya rage kudin hukumar kiyaye muhallin da kashi 31 cikin 100.

BBC ta fahimci cewar za a samo karin kudin da za a kashe a harkar tsaro bayan an rage kasafin kudin wasu fannonin.

Za a kara kudin ma'aikatar tsaron kasar da kashi 10 cikin 1000 kuma ma'aikatar tsaron cikin gida za ta samu karin kashi 6 cikin 100.

Kasafin kudin zai kunshi wata dala biliyan 1.5 na shirin farko na gini da kuma katangar da Trump ya yi alkawarin ginawa tsakaninshi da Mexico.

Fadar White House tana son ta rage kasafin kudin ma'aikatar makamashin kasar da kashi 30 cikin 100.

Ma'aikatar makamashin za ta iya samun gagarumin ragi a dakunan gwaje-gwajenta 17 wadanda suke bincike kan fannoni irin su makamashin nukiliya da kuma abubuwan samun makamashi da adana su da kuma amfani da su.

Za kuma a hana hukumar yada labaran kasar kudi. Hukumar ce irinta mafi girma da ke samar da kudin watsa shirye-shirye a Amurka.

Kasafin kudin, wanda aka yi wa lakabi da kasafi "mara tsoka" zai tsaya kan dala triliyan daya daga cikin dala triliyan 4 na kasafin kudin shekara-shekara da ake amfani da su wajen biyan kudin hukumomi da masana'antun Amurka.