Majalisa ta ce Hameed Ali ya koma ya sa kayan-sarki

. Hakkin mallakar hoto .
Image caption Shugaban hukumar fasa kauri ta Najeriya, Kanar Hameed Ali murabus

Majalisar Dattawan Najeriya ta umurci shugaban Hukumar hana fasa kaurin kasar, Kanar Hameed Ali murabus, ya koma ya sa kayan-sarki kafin ya bayyana a gabanta.

Wani zaman da mataimakin shugaban majalisar, Ike Ekwerenmadu ya jagoranta, ya umurci Hameed Ali ya dawo zaurenta ranar Laraba cikin kayan-sarki na Kwastam din.

Majalisar ta dau matakin ne ranar Alhamis bayan shugaban hukumar kwastam din ya bayyana a gabatanta cikin farin kaya.

Amma ba ta ba shi damar bayyana dalilin da ya sa ya ki saka kayan sarki ba.

Majalisar ta tiliasta wa shugaban ne kan ya zo, ya bayyana dalilin da ya sa hukumar tasa ta ce za ta fara karbar haraji kan motocin da aka riga aka shigar da su kasar, ba bisa ka'ida ba.