Nigeria: Kotu ta ce a tsare Andrew Yakubu kan miliyan $9.8

;. Hakkin mallakar hoto ENCYCLOPEDIA
Image caption Andrew Yakubu ya ce kudaden da aka samu a gidansa na kyauta ne

Wata Kotu a Abuja ta yi wa tsohon shugaban kamfanin man Najeriya, Andrew Yakubu, daurin wucen gadi kafin ta saurari neman belinsa a shar'iar da ake yi a kan dala miliyan 9.8 da aka samu a boye a wani gidansa.

Hukumar yaki da masu yi tattalin arzikin kasar ta'annati, wato EFCC , ta gurfanar da Andrew Yakubu gaban wata babbar kotun tarayyar Najeriyar ne a ranar Alhamis da laifukan da ke da alaka da halalta kudin haram, da rashin bayyana kadarori da kuma damfara.

Duk da cewar Andrew Yakubu ya amince cewar kudin da aka samu a wani gidansa da ke Kaduna nasa ne, ya ki amsa laifuffukan da ake tuhumarsa da su.

Alkalin kotun, Ahmed Mohammed, ya ce tunda Mista Andrew Yakubu ya ki amsa laifukan da ake tuhumarsa, zai ci gaba da kasancewa a hannun kotun.

Hakkin mallakar hoto .
Image caption .

Saboda haka Alkalin ya ba da umurnin a tisa-keyarsa zuwa gidan yarin da ke Kuje, a Abuja.

Lauyan da ke kare Andrew Yakubu, ya nemi kotu ta ba da belinsa cikin sauki domin mutumin da ake tuhumar ba shi da wani tarihin aikata laifi kuma ya dawo daga kasar waje domin taimaka wa hukuma kan binciken da take yi kan kudin da aka samu a gidansa.

Lauyan ya kuma nemi a ba da belin Andrew Yakubu domin ya samun damar fita kasar waje domin kula da lafiyarsa.

Amma ita hukumar EFCC ta nemi kotu ta yi watsi da bukatar lauyan Andrew Yakubu.

Ranar 21 ga watan Maris ne Andrew Yakubun zai sake bayyana a gaban kotun.