Yadda Boko Haram ta kashe mutum 291 a Niger

. Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Boko Haram ta fara tada kayar baya ne a Najeriya kafin ta fara kaddamar da hare-hare a Nijar da Kamaru da kuma Chadi

Majalisar Dinkin Duiya ta ce fararen hula 291 aka kashe kuma aka jikkata mutum 143 a hare-haren da aka daura alhakinsu kan 'yan Boko Haram da ke ikirarin jahadi a Najeriya.

An kai hare-haren ne cikin shekara biyu tsakanin watan Fabrairun shekarar 2015 zuwa Fabrairun 2017 a yankin Diffa da ke kudu-maso yammacin Nijar a kusa da Najeriya.

Shafin Intanet na ofishin dai-daita sahun ba da agajin Majalisar Dinkin Duniya (MDD) ya ce mutum 18 aka yi garkuwa da su, inda mutum uku suka bace.

Hukumar ta MDD ba ta bayyana adadin mayakan Boko Haram 'yan Najeriya da aka kashe ba.

An tabbatar da hare-hare mafi muni a kauyukan da ke kan iyakan Najeriya da kuma wasu wurare a tafkin Chadi.

Masu ikirarin jihadin sun kama garin Bosso da ke kan iyakan Nijar da Najeriya a watan Yunin shekarar 2016.

Hukumar dai-daita ba da agajin ta ce iyakar jihar Bosso da Najeriya na da kashi 70 cikin 100 na hare-haren inda aka kashe mutum 203 kuma mutum 44 suka jikkata yayin da aka yi garkuwa da mutum ukun kuma wasu ukun suka bace.

Wasu daga cikin wadanda abin ya rutsa da su sun shaida wa kamfanin dillancin labaran AFP cewar an kashe wasu ne ta hanyar harbi da kunar bakin wake da kuma yankan rago.

Kungiyar Boko Haram ta kai harinta na farko Kasar ne a ranar 6 ga watan Fabrairun 2015. Yan gudun hijira sama da 300,000 suke zaune a yankin na Diffa. Wadanda suke taimaka musu mazauna gurin ne wadanda su ma a cikin halin talauci suke.