Wales ta dauki matashin dan Liverpool Woodburn

Ben Woodburn a wasan Liverpool da Plymouth Argyle Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Ben Woodburn a lokacin wasan Liverpool da Plymouth Argyle a gasar Kofin FA ta bana

Matashin dan wasan Liverpool Ben Woodburn ya samu gayyatar shiga tawagar 'yan wasan Wales a karon farko, domin wasan neman gurbin gasar Kofin Duniya da Jamhuriyar Ireland, ranar 24 ga watan Maris.

Dan wasan mai shekara 17 ya buga wa Liverpool wasa har sau bakwai, a bana, kuma ya kasance dan wasa mafi karancin shekaru da ya ci wa kungiyarsa kwallo.

Dan wasan gaban, haifaffen yankin Nottingham ya cancanci buga wa Wales ta asalin kakansa na wajen uwa, kuma dama tuni ya buga wa tawagar Wales din ta 'yan kasa da shekara 16, da 'yan kasa da shekara 18, da kuma kasa da shekara 19 wasanni.

Gareth Bale da Aaron Ramsey ma na cikin tawagar bayan da suka murmure daga jinyar da suka yi.

Bale dan wasan gaba mai shekara 27 ya buga wa kungiyarsa ta Real Madrid wasa biyar, bayan da ya murmure daga ciwon idon sawu, wanda ya hana shi wasa tsawon wata uku.

Shi ma dan wasan tsakiya Ramsey, wanda bai buga wasa ba tsawon wata guda, saboda ciwon sharaba, ya yi wa kungiyarsa ta Arsenal wasa biyu na baya-bayan nan.

Tawagar Coleman din ta hada da, dan wasan gaba Tom Lawrence, wanda yaci kwallo 11 a tsawon zaman da ya yi a kungiyar Ipswich, a matsayin aro daga Leicester.

Wales tana mataki na uku a rukuni na hudu, wato Group D, da maki hudu tsakaninta da Jamhuriyar Ireland din wacce take ta farko a rukunin.