'Jami'an tsaro sun fara kama masu hannu a rikicin Ile Ife'

Ministan harkokin cikin gidan Najeriya Hakkin mallakar hoto facebook
Image caption Abdurrahman Danbazau ya ce ba za a kyale duk wanda aka samu na da hannu a rikicin ba

Wani bincike ya nuna cewa yanzu haka mutane guda biyar da ake zargi da kitsa rikicin Ile Ife wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane fiye da 30 na hannun jami'an tsaro.

Mutanen dai su ne:

  • Misis Kuburat
  • Escort Jagaban Sabo
  • Mista Abiodun
  • Damola
  • Jimoh.

Tuni dai gwamnatin kasar, ta ce za ta hukunta duk mutumin da aka samu da hannu a rikicin.

Ministan harkokin cikin gida, Abdurrahman Danbazau ne ya nanata hakan, yayin wata ziyarar gani da ido da ya kai Ile Ifen ranar Alhamis.

Da man dai gwamnatin Najeriya ta kafa wani kwamiti wanda yake bincike kan hakikanin abin da ya faru.

Abdurrahman Danbazau ya ce "Kuna garin nan kusan shekara dari biyu ke nan, kakannin kakanninsu nan aka haife su, to dan me za a ce rikici ne tsakanin Bahaushe da Bayarbe, ba haka ba ne."

Ya ci gaba da cewa "wannan rikici dai za a iya cewa wadannan kangararru masu zaman banza ne suka janyo shi."

"Muna yi muku alkawari cewa duk wanda aka samu da hannu a wannan rikici za a hukunta shi insha Allahu", in ji Danbazau.

Wannan dai kusan za a iya cewa shi ne karon farko da Hausawa da Yarabawa suka samu sabani a birnin na Ile Ife.

Kuma kamar yadda minista Abdurrahman Danbazau ya ce "Zauna gari banza" ne suka haddasa rikicin.

Yanzu dai abin da 'yan Najeriya musamman 'yan arewacin kasar ke zuba ido su gani shi ne, yadda za a hukunta masu hannu a fadan kabilancin na Ile Ife.

Labarai masu alaka

Karin bayani