'Mutane da yawa ba su san suna da makanta ba'

Glaucoma
Image caption Cutar Glaucoma na haddasa makanta a Najeriya

Wani bincike da aka yi kan cutar dusashewar gani wato Glaucoma, a Najeriya, ya nuna cewa mutane da dama na da cutar ba tare da sanin suna da ita ba.

Binciken dai ya nuna cewa kashi biyar cikin dari na masu shekara 40 zuwa sama, a kasar na da cutar.

Cutar ta Glaucoma dai tana cin idanuwa a hankali sannan daga bisani ta nakasa su.

Masu wannan matsala dai na farawa ne da rashin gani ta gefe.

Ku saurari Dr Fatima Kyari, wata kwararriyar likitar ido ce a Nigeria, wadda ta yi wa Yusuf Tijjani karin bayani kan girman matsalar cutar ta Glaucoma.

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Dr Fatima Kyari, kwararriyar likitar ido a Nigeria,