Harin masallaci ya kashe mutum 42 a Syria

Masallacin al-Jineh Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Masallacin al-Jineh ya ruguje

Mutum 42, wadanda akasarinsu fararen hula ne sun mutu sakamakon harin sama da aka kai kan wani masallaci a wani kauye da ke karkashin ikon 'yan tawaye a arewacin Syria.

Kungiyar kare hakkin dan adam dake sa ido a Syria ta ce harin wanda wani jirgin sama da ba a gane ko mallakin wacce kasa ba ne, ya je al-Jineh da ke yankin Aleppo.

Jiragen Rasha da na Syria na kai hare-hare yankin kuma jiragen saman Amurka na yaki ma na kai hari kan 'yan tawaye dake yankin.

Amurka ta ce ta kai harin sama, wanda ya yi sanadiyar mutuwar 'yan kungiyar al-Qaeda da dama amma bata kai hari kan masallaci ba.

Da farko dai dakarun Amurka sun ce harin ya auku ne a yankin Idlib, amma kuma daga baya sai suka ce basu da tabbacin inda aka kai harin.

Wani mai magana da yawun sojin Amurkan, kanar John J Thomas ya ce "Ba mu kai hari kan masallaci ba, amma mun kai kan ga wani gini inda aka yi ganawar, wanda ke da nisan mita 15 daga masallacin dake nan har yanzu.

Kungiyar sa ido dake Burtaniya, wanda ke karbar sakon jawabai daga majiyoyi dake Syria, ta ce mutane sun taru a masallacin domin yin sallar la'asar a lokacin da aka kai harin.

Image caption Harin Damascus din ya auku ne a ranar da aka cika shekara shida da fara bore a kan shugaba Basha al-Assad

Kauyen dai na daya daga cikin yankunan Syria da ke karkashin ikon 'yan tawaye.

Harin da aka kai a ranar Alhamis ya zo ne kwana daya bayan akalla mutum 31 sun mutu a wani harin kunar bakin wake a wani gini a Damascus, babban birnin kasar.

Harin Damascus din ya auku ne a ranar da aka cika shekara shida da fara bore a kan shugaba Basha al-Assad.

Wasu masu fafutuka sun ce, tun daga lokacin, an kashe sama da mutum 320,000 kuma wasu miliyan 11 sun rasa muhallansu sakamakon rikicin.

Labarai masu alaka