Sojojin Najeriya hudu sun mutu wajen yaki da Boko Haram

Sojan Najeriya Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Lamarin ya faru ne a yayin wani hari da 'yan bindigar suka kai a garin Magumeri da ke jihar Borno

Rundunar sojin ruwa ta Najeriya, ta ce sojojinta hudu sun mutu a wani artabu da aka yi tsakaninsu da wasu masu dauke da bindiga da ake zargin 'yan kungiyar Boko Haram ne.

A wata sanarwa da ta fito daga rundunar sojin kasar ta fitar, kakakinta rundunar, Birgediya janar Sani Usman Kuka Sheka ya ce, akalla sojojin Najeriya hudu ne da kuma wani jami'in dan sanda suka rasa rayukansu a yayin harin.

Lamarin ya faru ne a yayin wani hari da 'yan bindigar suka kai a garin Magumeri dake jihar Borno a arewa maso gabashin kasar.

Sanarwar ta ce kawo yanzu ba a san inda wasu sojojin uku suka shiga ba, bayan dakaru sun fatattaki maharan da ake zargin 'yan Boko Haram ne daga garin Magumeri da kuma wasu kauyuka biyar.

Rundunar ta kuma ce ta karya lagon wasu 'yan Boko Haram da bata bayyana adadinsu ba, sannan ta kwace wasu muggan makamai daga hannunsu da suka hada da rokoki da bindigogi masu sarrafa kansu da albarusan makamai masu kakkabo jiragen sama da abubuwan hada bama-bamai da kuma kayan abinci.

Ta kuma kara da cewa wasu sojoji sun yi batan damo a lokacin harin da aka kai a ranar Talata da daddare.

Sojojin kasar dai na ci gaba da ikirarin samun galaba a kan kungiyar ta Boko Haram amma wasu 'yan kasar na ganin jami'an tsaro na da sauran aiki a gaba, ganin irin hare-haren da 'yan kungiyar ke ci gaba da kaiwa a ciki da kuma wasu kasashe makota.

Labarai masu alaka