'Yan cirani 31 sun mutu a tekun Yemen

Taswira
Image caption Ba a bayyana wadanda suka ka kai harin ba.

Majalisar dinkin duniya ta ce 'Yan ciranin kasar somaliya da dama sun rasa rayukansu a lokacin da aka kai wani harin sama a kusa da gabar tekun Yemen.

Kafofin yada labarai sun amabato jami'an tashar jiragen ruwan Hudaydah na cewa akalla mutum 31 ne suka mutu a harin.

Hutuna sun nuna gawarwarkin mutane a baje a cikin jirgin ruwa.

Wani mai tsaron gabar takun, Mohammed al-Alay ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa, 'Yan ciranin dai na hanayar su ne ta zuwa Sudan daga Yemen a lokacin da wani jirgi mai saukar ungulu ya kai musu harin.

Sai dai ba a bayyana wadanda suka kai harin ba.

'Yan tawayen Houthi, wadanda ke fada da rudunar kwance da Saudiya a yakin Yemen da aka kwashe shekara biyu ana yi ne dai ke da ikon tashar jiragen ruwan.