Pakistan na son Facebook ta taimaka wajen yakar batanci

'Yan pakistan Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Furta kalaman batanci babban laifi ne a Kasar Pakistan.

Kasar Pakistan ta nemi shafin sada zumunta na Facebook ya taimaka wajen binciken yada ababen batanci.

Kasar Pakistan ta ce ta bukaci shafin sada zumuntan ya taimaka wajen binciko "kalaman batanci" wadanda 'yan kasar Pakistan ke yadawa a shafukan na Facebook.

A cewar Ministan cikin gidan kasar, Chaudhry Nisar, ya ce kasart Pakistan za ta yi duk abinda da ya kamata wajen kawar da matsalar yada kalaman batanci kan sfukan sada zumunat

Furta kalaman batanci babban laifi ne a Kasar Pakistan. Babu takamamman bayani kan me ka iya zama batanci a kasar. A baya dai kalaman zarge-zargen batanci ne kan zanen Annabi Muhammad (SAW) da kuma suka kan ayoyin Alkur'ani.

Masu suka sun ce, dokar furta kalaman batanci wacce ta ba da damar hukuncin kisa a wasu lokutan, sau da yawa ana yin amfani da ita wajen zaluntar 'yan tsiraru.

A farkon makon nan ne dai Firai ministan Kasar Pakistan, Nawaz Sharif, ya nuna goyon bayansa a kan aiwatar da dokar furta kalaman batanci kan masu amfani da shafukan sada zumunta.

A wani bayani da ya yi a shafin Twitter na jami'an jam'iyyarsa, ya bayyana kalaman batanci a matsayin laifin da ba za a barshi ba.

A ranar Alhamis, Ministan cikin gida, Chaudhry Nissar, ya kara tabbatar da ikirarin Kasar Pakistan don fuskantar lamarin,inda ya ce zai dau duk wasu matakan da suka dace don tabbatar da sakon Kasar ta Pakistan ya shiga ko'ina.

Ya bukaci jami'ai da hukumar bincike na Kasashen Amurka da shafukan sadarwa su rinka kula da dandalin akai-akai.

Jaridar Dawn ta ambato shi yana neman shafin Facebook da sauran shafuka su bayar da bayanai kan mutanen da ke kalaman batanci.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Kasar Pakistan ta toshe shafukan batsa da shafin Kungiyar 'yan ta'adda.

A shekarar 2010 ne kotun Kasar Pakistan ta rufe shafin Facebook a kan batancin da akai wa Annabi Muhammad (SAW).

Labarai masu alaka