Za mu gyara asibitocin Najeriya guda 70 — NHIS

Hukumar inshorar lafiya ta Naijeriya NHIS Hakkin mallakar hoto Getty Images

Yayin da wasu masu ruwa da tsaki ke nuna damuwa a kan lalacewar cibiyoyin lafiya a Najeriya musamman manyan asibitocin gwamnatin tarayya, hukumar inshorar lafiya ta kasar ta dauki aniyar kawo gyara a bangaren.

Rahotannin sun ce akasarin asibitocin kasar na fama da matsalar halin ko-in-kula da karancin kayan aiki, da sauran abubuwan da suka shafi kiwon lafiya.

Hakan dai na kawo cikas wajen kokarin inganta lafiyar al'umma.

Hukumar inshorar lafiya ta Nijeriya wato NHIS,ta ce za ta fara gyara wasu daga cikin manyan asibitocin kasar a wani mataki na inganta lafiyar jama'a.

Babban sakataren hukumar, Farfesa Usman Yusuf ya shaida wa BBC cewa akwai asibitocin kasar da dama da ba sa iya yin aikin tiyata, saboda rashin ingantattun kayan aiki.

Ya kuma ce mata masu juna biyu da kananan yara ba sa samun kyakkyawar kulawa a irin wadannan asibitoci.

''Manya-manyan asibitoci 56, da kananana 14 muke so mu taimaka wa a cikin wannan asusun da muka tara kudin jama'a.''

Tallafin dai zai shafi yadda za a taimaka wa masu fama da cutar yoyon fitsari da masu cutar noma.

Farfesa Yusuf ya kuma kara da cewa tallafin da za su bayar ya danganta ga girman asibiti da kuma bukatun da suka gabatar.

Labarai masu alaka