Nigeria: An rusa gidajen mazauna gabar teku 4000 a Lagos

A map of Nigeria, showing the Lagos region in relation to the capital, Abuja

Kungiyoyin kare hakkin dan'adam a Najeriya sun ce 'yan sanda sun rusa gidaje na fiye da mutum dubu hudu a wani yanki da ke gabar tekun, a cikin birnin Lagos na Kudancin kasar.

Kungiyoyin sun ce matakin na 'yan sandan ya keta wani umarnin kotu, wadda ta ce kamata ya yi su shiga tsakani domin sasantawa da al'ummar yankin.

Shaidu sun ce rikici ya barke lokacin da motocin ture gine-gine suka bayyana a yankin Otodo-Gbame inda masunta ke zama, da safiyar ranar Juma'a.

Rahotanni sun ce 'yan sanda sun yi amfani da alburusai da hayaki mai sa hawaye wajen tarwatsa masu gidajen da suka rirrike hannuwan juna a kokarinsu na hana rusa musu matsugunnai.

Masu kare hakkin dan adam din sun ce, wannan almari ya jawo kimanin mutum 4,700 sun rasa matsugunnai a yanzu haka.

Megan Chapman ta wata cibiyar da ke kokarin tabbatar da adalci, wadda ke aiki da al'ummar yankin, ta shaida wa BBC cewa, "an lalata kusan komai a wajen, wadanda rabinsu a kan ruwa suke."

Ya zuwa yanzu dai rundunar 'yan sandan Najeriya ko gwamnatin jihar Lagos ba su ce uffan ba tukunna.

Amma a baya gwamnatin jihar ta sha cewa 'Tana lura sosai wajen kare hakkin al'ummar da ke yankin."

A watan Nuwambar 2016 ne gwamnatin jihar Lagos ta yi watsi da zargin da aka yi cewa, ta fara yunkurin korar mazauna wajen, wadanda ta ce ba bisa ka'ida suke zaune a yankin ba.

Mazauna wannan yankin dai sun kai kusan shekara dari suna rayuwa a wajen, tun kaka da kakanni.

Labarai masu alaka

Karin bayani