Hotunan abubuwan da suka faru a Afirka a makon nan

Ga wasu hotuna da aka zabo na abuuwan da suka faru a nahiyar Afirka cikin makon nan.

Wani ma'aikaci a wajen baje-kolin ganyen taba a Harare, babban birnin kasar Zimbabwe, yana dudduba tabar a wajen taron na 2017 da ake yi. An dauki wannan hoto ne ranar Laraba. Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Wani ma'aikaci a wajen baje-kolin ganyen taba a Harare, babban birnin kasar Zimbabwe, yana dudduba tabar a wajen taron na 2017 da ake yi. An dauki wannan hoto ne ranar Laraba.
Wannan hoton yadda sojojin fadar shugaban kasar Kenya suka yi wa shugaba Uhuru Kenyatta faretin girmamawa nea ranar Laraba, kafin ya gudanar da jawabinsa ga majalisar kasar. Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wannan hoton yadda sojojin fadar shugaban kasar Kenya suka yi wa shugaba Uhuru Kenyatta faretin girmamawa a ranar Laraba, kafin ya gudanar da jawabinsa ga majalisar kasar.
Yadda wani ya shafe jikinsa da fenti don murnar wannan rana. Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Haka kuma a ranar Larabar ne dai 'yan kasar Laberiya suka yi bikin tunawa da ranar haihuwar shugaban kasar na farko Joseph Jenkins Roberts, wanda aka haife shi a shekarar 1829.
Shugaban Rasha Vladimir Putin tare da ministan harkokin kasashen waje Sergei Lavrov da kuma mai bai wa shugaban shawara Yury Ushakov su ne suka tarbi sabon jakadan na jamhuriyyar Benin. Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaba Vladimir Putin na Rasha ya yi wa sabon jakadan jamhuriyyar Benin maraba da zuwa kasar, a wani dan karamin biki a fadar Kremlin a ranar Alhamis.
Wani dan kasar Masar da ya dauki hutun aiki a ranar Litinin, don ya kasance cikin wadanda za su daga mutum-mutumin Fir'auna da aka tono a karkashin kasa a birnin Alkahira. Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wani dan kasar Masar da ya dauki hutun aiki a ranar Litinin, don ya kasance cikin wadanda za su daga mutum-mutumin Fir'auna da aka tono a karkashin kasa a birnin Alkahira.
Dumbin mutane ne suka taru don yin wadannan addu'o'i a Juba. Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Wannan wani fasto ne na Sudan ta Kudu, da ya jagoranci yin addu'o'i na neman tuba da gafara ga kasar, a ranar Juma'a a Juba, babban birnin kasar.
A watan da ya gabata ne aka ayyana cewa Sudan ta Kudu na fama da matsanancin fari. Wata hukumar kula da 'yan gudun hijira ta kasar Norway ce ta raba masara da wake da gero a jihar. Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption A wannan ranar ta Juma'a ce dai kuma mata suka karbi taimakon abinci a jihar Unity ta Sudan ta kudun, inda ake fama da matsanancin fari.
A ranar Lahadin kuwa dumbin mutane ne suka taru don kallon yadda ake aikin ceto wadanda bola ta danne a Addis Ababa, babban birnin Habasha. Hakkin mallakar hoto AP
Image caption A ranar Lahadi kuwa dumbin mutane ne suka taru don kallon yadda ake aikin ceto wadanda bola ta danne a Addis Ababa, babban birnin Habasha.
Fiye da mutum 100 ne suka mutu a ifti'a'in da ya faru, kuma a ranar Litinin ne aka yi jana'izar wasu daga cikin mutanen da suka mutun. Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Fiye da mutum 100 ne suka mutu a ifti'la'in da ya faru, kuma a ranar Litinin ne aka yi jana'izar wasu daga cikin mutanen da suka mutun.
Shugaba Buhari ya shafe kwana 50 a London. Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption A ranar Juma'a kuwa shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ne ya dawo gida Najeriya bayan dogon hutun jinya da ya yi a Birtaniya. An tarbi shugaban cikin walwala a Abuja babban birnbin kasar.
A ranar Alhamis ne shugaban Masar Abdel Fattah al-Sisi ya yi wa wani dan kasar afuwa, bayan da a baya aka daure shi saboda samun sa da hannu cikin shirya zanga-zanga. Jama'a sun taru don yi masa murna a gaban gidan yari aTora. Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption A ranar Alhamis ne shugaban Masar Abdel Fattah al-Sisi ya yi wa wani dan kasar afuwa, bayan da a baya aka daure shi saboda samun sa da hannu cikin shirya zanga-zanga. Jama'a sun taru don yi masa murna a gaban gidan yari aTora.
Mutane a Antananarivo, babban birnin Madagascar suna diban ruwa a wani yanki da aka yi ambaliya sakamakon guguwar Enawo da aka yi. An dauki hoton a ranar Juma'a. Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Mutane a Antananarivo, babban birnin Madagascar suna diban ruwa a wani yanki da aka yi ambaliya sakamakon guguwar Enawo da aka yi. An dauki hoton a ranar Juma'a.
Wani tsuntsu mai dogon baki yana kare kansa daga wani mai daukar hoto a Nairobi, babban birnin kasar Kenya a ranar Asabar. Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wani tsuntsu mai dogon baki yana kare kansa daga wani mai daukar hoto a Nairobi, babban birnin kasar Kenya a ranar Asabar.

An samu hotunan ne daga kamfanonin dillancin labarai na AFP da EPA da Getty Images da kuma Reuters

Labarai masu alaka