Boko Haram ta kassara cinikin burodi a Maiduguri

Gidan burodi a Maiduguri
Image caption Gidajen burodi da dama sun mutu a Maiduguri saboda hare-haren Boko Haram

Hare haren Boko Haram sun yi mummunan tasiri kan gidajen burodi a ciki da wajen birnin Maiduguri na jihar Borno, arewa maso gabashin Najeriya

Gidajen burodi na cikin wuraren da Boko Haram ta rika kai hare-hare tare da hallaka ma'aikatansu har ma da masu sayar da shayi a ciki da wajen birnin.

Kuma duk da kwanciyar hankalin da birnin Maiduguri ke ci gaba da samu, harkokin gidajen burodi har yanzu suna cikin garari, inda matasa da yawa da suka saba aiki a gidajen burodin ke zaman kashe wando.

Wasu masu sana'ar burodin sun shaida wa BBC cewa duk da kwanciyar hankalin da ake samu a birnin Maiduguri, har yanzu kasuwancin burodin ya tsaya cak.

Image caption Matasa da dama na zaman kashe wando a gidajen burodi a Maiduguri saboda koma ya tsaya

Malam Lawan Dan Gashua jami'in hulda da jama'a na kungiyar masu gidan burodi shiyyar arewacin Najeriya ya ce baya ga hare haren Boko Haram da suka faru a baya, tsadar kayan sarrafa burodi kamar fulawa da sukari sun kara durkusar da sana'arsu.

A cewarsa ɗumbin gidajen burodi a yanzu sun mutu saboda rashin kasuwa.

Ya ce kafin sojoji su fatattaki mayakan na Boko Haram daga birnin, 'yan tada-ƙayar-bayan sun kona gidajen burodi tare da hallaka mutanensu da dama.

''An kashe mana mutane da yawa, a gaba na an kashe mutane 11, an kashe masu shayi ba a san iyakarsu ba''.

Malam Abdulrahaman manajan gidan burodin 'Umar Butter Bread' da a baya ke da daruruwan matasa da ke aiki a wurin, ya ce yanzu harka ta lalace, babu kasuwa.

'' A da ina juye fulawa daga buhu daya zuwa tamanin, amma yanzu ban isa in juye buhu talatin ba, kuma a da mutane sukan yi tururuwa su kawo kudin burodi don kada ya kare (amma yanzu sai tashin zance).''

Labarai masu alaka