Talakawa sun watsa wa Firayim-Ministan Lebanon tumatir

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Sa'ad Hariri ya zama Firayim-Ministan Lebanon a watan Disamban 2016

Rahotanni daga kasar Lebanon na cewa na jefi Firayim-ministan kasar, Sa'ad Hariri, da gorunan ruwa na roba da kuma tumatiri lokacin da yake jawabi ga masu zanga-zanga wadanda suka fusata saboda da shirin kara kudin haraji.

Mista Hariri ya shaida wa masu zanga-zanga su kimanin dubu daya, wadanda ke dauke da kwalaye a birnin Beirut, cewa zai kasance daram tare da su wajen yaki da cin hanci da rashawa.

To amma ala tilas ya gudu ya shiga motarsa yayin da masu zanga-zangar ke eho suna cewa 'barawo!', 'ba za mu biya harajin ba''.

A halin yanzu dai majalisar dokokin Lebanon na duba wasu shawarwari na kara kudaden haraji, ciki har da karin harajin cinikin kayakin masarufi da kashi daya cikin dari.