Wata ƙatuwar bishiya ta kashe mutum 18 a Ghana

Wurin yawon bude ido na Kintampo a kasar Ghana Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Bishiyar ta yanko da fada kan mutanen da ke ninkaya a ruwan da ke gangarowa daga tudu

'Yan sanda a kasar Ghana sun ce mutane akalla 18 ne suka mutu, lokacin da wata katuwar bishiyar ta faɗa musu yayin wani mamakon ruwan saman da aka sheƙa a yammacin ranar Lahadi

Mutane fiye da 25 ne kuma aka bayyana cewa sun jikata a hatsarin wanda ya faru a wani tudu da ruwa ke gangarowa na yankin Kintampo.

Mutanen da abin ya shafa suna cikin ninkaya ne a ruwan da ke gangarowa daga tudun, wanda daya ne daga cikin wuraren da masu yawon bude ido suka fi ziyarta a Ghana.

Hukumonin a kasar ta Ghana sun ce akasarin wadanda lamarin ya rutsa da su dalibai ne da ke ziyayar karin ilmi da yawon bude ido a wannan wurin shakawata na Kintampo.

Akwai alamun cewa wasu karin mutanen na makale karkashin ruwan.

Hakkin mallakar hoto Google
Image caption Akasarin wadanda hadarin ya rutsa da su dalibai ne

Masu aikin ceto na kokarin zakulo wadanda me yiwuwa ke da sauran numfashi bayan da dare ya tsala.

Mai magana da yawun hukumar kashe gobara ta kasar Ghana Prince Billy Anaglate ya shaidawa manema labarai cewa lamarin ya faru ne a yankin Brong-Ahafo .

Ya kuma shaidawa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa dalibai 18 sun mutu nan take a wurin, yayinda sauran biyu suka mutu a asibiti.

Wata tawagar jami'an yansanda da ma'aikatan kwana-kwana na ta kokarin ceto wadanda me yiwuwa ke da sauran shan ruwa.

Ya kuma ce ana yiwa wasu 11 magani, da suka hada da daya daga cikin malaman da ke jagorantar daliban.

Wasu rahotanni kuma sun bayyana cewa adadin wadanda suka jikkata ya haura 20, kuma ana duba lafiyarsu a asibitin yanki na Kintampo.

A wata sanarwa ministar harkokin yawon bude ido ta kasar Ghana Catherine Abelema Afeku, ta nuna jimaminta tare da yi wa 'yan'uwan wadanda lamarin ya rutsa da su jaje da ta'azaiyya.

Labarai masu alaka