Injiniyan da ya kasa samun aiki don sunansa 'Saddam Hussain'

shugaban Iraki Saddam Hussein na yi wa magoya bayansa jawabi a Bagadaza a 1995 Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Saddam Hussein dai ya dade da mutuwa amma mafiya yawan takawrorinsa na fuskantar tsangwama

Fiye da shekara 10 kenan da kashe tsohon shugaban kasar Iraki Saddam Hussein, amma har yanzu yana da matukar tasiri a kan rayuwar wani mutum.

Wani Injiya a bangaren fasahar jiragen ruwa a Indiya, bai taba jin zargin ko jin haushin kakansa da sanya masa sunan tsohon shugaban Iraki shekaru 25 da suka gabata ba.

Bayan kin daukarsa aiki har sama da sau 40, a yanzu dai ya gane kamfanoni ba sa son daukarsa aiki ne kawai, duk da cewa akwai dan bambanci a sunansa da na tsohon shugaban Irakin, inda shi Hussain yake rubutawa a sunansa, ba Hussein ba kamar na tsohon shugaban.

Wannan dalili ne ya sa ya garzaya kotu domin sauya sunansa zuwa Sajida. Sai dai ana ta bata lokaci a cuku-cukun sauya masa sunan - wanda hakan ke kara jawo tsaiko ga samun aikinsa.

Shekara biyu bayan kammala digirinsa a jami'ar Noorol Islam ta Tamil Noorul, mutumin dan garin Jamshedpur a yankin Jharkhand, yana jin takaicin wannan lamari da yadda yake shafar rayuwarsa.

Ya samu sakamakon karatu mai kyau, kuma tuni abokan karatunsa sun riga sun samu aiki, amma kuma shi kamfanonin jiragen ruwa sun yi watsi da shi.

Wata jaridar Hindustan Times ta ambato Saddam wanda ya maida sunansa Sajid, yana cewa, "Mutane suna fargabar dauka ta aiki".

Ya ce suna tsoron matsalolin da za su fuskanta ne, da jami'an shige da fice a kan iyakokin kasashen duniya.

Saddam ya zaci zai samu saukin wadannan wahalhalun, idan ya sauya fasfo dinsa, da lasisin tukinsa da sauransu.

Amma har yanzu takardunsa na neman aiki basa samun karbuwa kamar yadda ya dace, saboda bai kawo hujja mai tabbatar da ya yi karatu da sabon sunan ba, kuma hakan ba karamin jan lokaci yake ba.

Wata kotu ta sanya ranar biyar ga watan Mayu, don ci gaba da sauraron karar, da kuma tilasta wa hukumomi su sauya masa suna a takardun kammala karatunsa na Sakandire da na jami'a.

Ba Sajid ne kadai ke fuskantar wannan tsangwama ba, amma watakila ya fi fuskantar tarnaki fiye ma da sauran masu suna Saddam Hussein da dama a Iraki, wandanda ke jin cewa ana la'antarsu ne, saboda sanya musu sunan da ya samo asali daga tsohon shugaban da ake ganin ya yi mulkin kama karya.


'Masu suna Saddam basu tsira ba ko a Iraki'

Wani dan jarida mai suna Saddam, wanda yake aiki a Ramadi, wani birni na 'yan Sunni a Lardin Anbar, ya ce an kori Babansa daga aikin gwamnati, saboda ya kasa gamsar da shugabanninsa cewa shi ba dan Jam'iyyar Ba'ath ba ne, ta tsohon shugaban kasar.

Sun ce idan babu wata alaka mai karfi tsakaninsa da hambararren shugaban kasar, wanne dalili ne ya sa shi sanyawa dansa suna Saddam Hussain.

Akwai labarai masu tayar da hankali game da wasu kan irin wannan lamari.

Wani kuma mai irin sunan ya ce sojojin Shi'a ne suka kama shi, suka durkusar da shi a kan gwiyoyinsa, kuma suka sanya masa bindigogi a kansa, suka ba shi wahala sannan suka sake shi.

Wani abokina ya shaida min yadda wani yaro dan makaranta, a Bagadaza wanda dan kabilar Kurdawa ne, ya san wani dan ajinsu mai suna Saddam Hussein da ya sha tsangwama a wajen mutane.

A lokacin da suke wasan kwallo a makaranta sai yaran su rika yi masa tsawa suna cewa, "ba wai mu kadai ba ne muka tsaneka, duk kasar nan sun tsaneka."

Labarai masu alaka