Shin Norway ce kasar da ta fi farin ciki a duniya?

Norway Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption 'Yan Norway na farin ciki a gasar kwallon kasa na shekarar 2009

Wani rahoton da Majalisar Dinkin Duniya ta fitar na nuna cewa kasar Norway ce kasar da aka farin ciki da murna a duniya, inda ta wuce makwabciyarta Denmark .

Rahoton farin ciki na duniya na auna ra'ayin mutane ne a kan yadda mutane ke samun farin ciki kuma dalilin da ya sa.

Kasashen Denmark da Iceland da Switzerland da kuma Finland na daga cikin kasashbiyar din da aka fi samun farin ciki, yayin da Jamhuriyar Tsakiyar Afrika ta zo karshe, in ji rahoton.

Yammacin Turai da Arewacin Amurka na sama a kan tebur na kasashe masu farin ciki, yayin da Amurka ke matsayin ta 14 da kuma Britaniya ta 19.

Kasashen da ke yankin Kudu da hamadar Saharar Afrika, da wadanda ke fama da rikice-rikice na daga can kasa a tebur din.

Syria ta na matsayin ta 152 daga cikin kasashe 155, yayin da Yemen da Sudan ta Kudu da ke fama da yunwa suka zama na 146 da 147.

An bayyana Kasashen duniya masu farin cikin yayin da ake bikin ranar da Majalisar Dinkin Duniya ta ware ta farin ciki wato 20 ga watan Maris.

Kasahen duniya masu farin ciki da masu bakin ciki
Masu farin ciki Masu bakin ciki
1. Norway 146. Yemen
2. Denmark 147. Sudan ta Kudu
3. Iceland 148. Laberiya
4. Switzerland 149. Guinea
5. Finland 150. Togo
6. Netherlands 151. Rwanda
7. Canada 152. Syria
8. New Zealand 153. Tanzaniya
9. Australiya 154. Burundi
10. Sweden 155. Jamhuriyar Tsakiyar Afirka

Wannan rahoto ya dogara ne a kan tambayar da ake yi game da rayuwar mutane fiye da 1000, a ko wace shekara a kasashe fiye da 150.

Tambayar ita ce, ''Ka yi tunanin ga wani tsani nan da lambobi, daga kasa lambar 0 zuwa lamba 10 a sama.''

''Lambobin saman tsanin ne ke nuna cewa rayuwa ta yi armashi a wajenka, yayin da na kasan tsanin ke nuna rayuwa ta yi muni. Don haka za ka zabi lambar da ka ke ganin ta dace da yanayin rayuwar da ka ke ciki a wannan lokaci."

Amma rahoton yayi kokarin tantance bincike domin bayanin dalilin da ya sa wasu kasashe ke samun farin ciki fiye da wasu.

Binciken ya lura da dalilai da suka hada da karfin tattalin arzikin kasar da goyan bayan zamantakewa da tsawon rayuwa da 'yancin zabi da kirkin 'yan kasa da kuma karancin matsalar cin hanci da rashawa a kasar.

'Da sauran rina'

Sai dai masu sharhi da dama na ganin da sauran rina a kaba dangane da wannan rahoto, inda suke tababar ko Norway ta cancanci zama kasar da ta fi ko wacce farin ciki a duniya.

Saboda akwai wani rahoto da aka fitar inda Norway ta kasance kasa ta 19 da mutanen kasar suka fi kashe kansu.

A ganin masu sharhi, hakan zai zama wani babban koma-baya ga samun farin ciki a kasar, don idan har farin ciki ya yawaita a kasa, to bai kamata kuma a dinga samun yawan kashe kai da mutane ke yi ba.

'Rikicin kasar Amurka''

Rahoton wannan shekara na kunshe da wani take na, ''Sake kawo farin ciki a Amurka'', inda aka yi nazarin dalilin da ya sa farin ciki a Amurka ke raguwa duk da cewa kullum tattalin arzikin kasar na inganta.

Marubutan sun bayyana cewa, ''Amurka ta iya kuma ya kamata ta kara farin cikin 'yar kasarta ga magance rikicin zamantakewa da kasar ke fama da shi. Kasar ta mai da hakali a kan rashin daidato da cin hanci da kadaici da kuma shakka, maimakon mayar da hankali musamman a kan tattalin arzikin kasar.

'A takaice dai rikicin Amurka na zamantakewa ne, ba na tattalin arziki ba.'

Daraktan kungiyar samar da hanyar ci gaba mai dorewa, Jeffrey Sachs, wanda ya buga wannan rahoto ya ce manufofin shugaba Donald Trump kan iya sa abubuwa su yi muni.

Mista Sachs ya bayyana wa kamfanin dillacin labarai na Reuters cewa, ''Dukkan manufofin na kara rashin daidaito ta hanyar rage haraji da cire mutane daga tsarin kiwon lafiya da rage dawainiya da ake yi ta fuskar abinci domin kara kudaden ta hayar tsaron kasar. Ina ganin duk shawarwarin da ya bayyana basu dace ba.''

Rahoton ya nuna cewa aikin gwamnati na daya daga cikin abin da ke kara farin ciki maimakon aikin karfi amma samun aikin shi ne matsalar.

''A yayin da wadanda ke da aikin mai biyan albashi mai yawa na da farin ciki kuma sun gamsu da rayuwansu'' sakamakon ita ce'' karin dala 100 a albashi na da daraja ga wadanda ke samun albashi kasa da hakan fiye da wadanda suka riga suna samun albashi fiye da hakan.''

An shafe shekara biyar kenan ana fitar da wannan rahoto, inda kasashen yankin Arewacin Turai ke kasancewa a saman teburin ko yaushe.

Labarai masu alaka

Karin bayani