China za ta yi maganin barayin toli fefa a bandaki

Hoton ma'ajiyar toli fefa a wurin shakatawar "Temple of Heaven Park" da ke garin Beijing.
Image caption Injinan ba a kunne suke ba lokacin da BBC ta kai ziyara bandakunan a ranan Litinin

Wani wurin shakatawa a Beijing ya dasa ijinan ajiye tole fefan dake daukar hoton fuskokin mutune ta yadda mutum ba zai iya komawa a kai a kai yana diba ba.

Kafar watsa labarai ta rawaito cewa, wani wurin shakatawa a garin Beijing ya kawo injin tole fefa don hana masu kawo ziyara sata.

Injinan dake wurin shakatawa mai suna "Temple of Heaven Park " na daukar hoton fuskar wanda zai diba kafin yaba da damar cirar tole fefan.

An sha ba da rahoton masu yawon bude ido dake kai ziyara wurin shakatawar na kwasar tole fefan su tafi da shi gida.

Ya kuma tayar da muhawara a kan rashin yardar jama'a a cikin wasu 'yan kasar china.

jami'an gurin shakatawar sun makala injinan shida a bandakunansu wanda za su yi gwaji na makonni biyu, kuma ma'aikatan na yi wa baki karin bayani kan yadda ake amfani da na'urar.

An saka injinan ne ta yadda tsayin mutane zai iya kaiwa har su cira a lokacin da suke bukata.

Injin na bayar da fallen tole fefa guda a lokaci, idan har mutum yana bukatar kari to sai dai bayan mintuna 9 zai iya komawa ya kuma cirar wata.

Wani mai magana da yawun ma;akatan wurin shakatawan ya ce " idan muka samu bakon da yake fama da gudawa ko makamancin haka wanda suke bukatar toli fefa cikin gaggawa , ma'aikatanmu za su kawo musu cikin hanzari".

Image caption An ya yi alama a kan injin ,inda ya bukaci wanda ya kawo zai yi amfani da shi ya cire tabarau da hularsa don a haska fuskarsa.

Har'ila yau wurin shakatawar ya kara kyautata ingancin toli fefa wajen kara kaurinsa.

A lokacin da BBC ta kai ziyara bandakunan ranar Litinin, an kashe injinan. Daya daga cikin ma'aikatan ya ce an kashe injinan ne saboda babu baki dayawa a wurin shakatawar a wannan ranar.

Wawoso

A farkon watan nan ne, kafar watsa labaran china ta ba da rahoton cewa bakin da suke zuwa bandakunan wurin shakatawar sun ce ana karbar kudin toli fefa daga wurinsu da ya wuce kima, wasu daga cikinsu ma suna ganin ana shake musu jakankunansu

Wurin shakatawar ya shafe tsawon shekaru yana fama da wannan matsalar, bayan da suka fara bayar da tole fefan kyauta a shekarar 2017.

Hakkin mallakar hoto AFP/Getty Images
Image caption Wurin shakatawar da aka fi sani da "Temple of Heaven Park" na raba kyautar tole fefa.

Sun manna kyalleya masu dauke da sakonnin a kan tsarin da kuma fadakarwa a kanrage amfani da tole fefa.

An dai fara samun nasara saboda wurin shakatawar ya shaidawa Wanbao dake garin Beijing cewa sun samu ragin kashi 20 na kudin da suke kashewa a tole fefan na kowacce rana.

Kafar watsa labaran Beijin ta ce ,injinan biyu sun lalace kwanan nan lokacin a karshen mako.

Amma a wani bangaren kuma injinan sun zama wanni abu da ke jan hankulan mutane.

Wani mai shara a wurin ya shaidawa BBC cewa ,a baya ana fuskantar matsalar sace tole fefa sakamakon amma samun sabon injin na nufin idan mutane suka zo ba damar dauka sai dai su kalla.

Labarai masu alaka

Karin bayani