Kada ya kashe wani mutum a Australia

Wani kada a cikin ruwa Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Mutuwar mutumin zai iya kasancewa shi ne karo na tara da Kada ke kashe mutum a garin Queensland tun shekarar 1985

Hukumomi a Australiya sun ce sun gano gawar wani mutum wanda ake zargi Kada ne ya kashe shi a kasar.

An yi amannar mutumin, mai shekara 35, masunci ne wanda aka gano jirgin ruwansa ba komai a ciki, a kusa da Palmer Point a garin Queensland da ke Arewa mai nisa a ranar Asabar.

'Yan sandan Queensland sun ce wani bincike da aka gundanar tun da farko, ya gano cewa Kada ne ya kashe mutumin.

A ranar Lahadi ne Kada ya kai wa wani dan shekara 18 hari a garin Innisfail da ke kudancin kasar.

'Yan sandan da ke bincike a kan mutuwar mutumin sun ce sun fara neman Kadan mai tsayin sama da mita hudu.

Idan har aka tabbatar cewa Kadan ne yayi sanadiyar mutuwar mutumin, zai zamo karo na tara kenan da Kada ke kashe mutum a garin Queensland tun shekarar 1985.

Hukumomi sun ce a daren ranar Lahadi ne dai wani babban Kada ya tunkaro wani jirgin ruwan 'yan sanda cikin sauri kuma a fusace.

Image caption 'Yan sanda za su kashe ko su tsare Kadan idan suka gano shi

"Akwai yiwuwar wannan Kadan ne ke da alhakin mutuwar mutumin, in ji Dakta Matt Brein na ma'aikatar kare Muhalli da Al'adu.

Za a kashe shi ko a tsare shi idan har aka gano Kadan.

Labarai masu alaka