Bankin duniya zai bai wa Afirka da $57bn

. Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Taimakon na bankin duniya zai mayar da hankali ne kan ayyukan samar da ababen mre rayuwa da ilimi da da samar samr da tsaftaceccen ruwa.

Bankin Duniya ya bayar da sanarwar gabatar da wani shiri na samar da kudaden raya kasa na shekara uku a kasashen Afirka dake Kudu da hamada, wanda yawansu ya kai dala biliyan hamsin da bakwai.

Galibi dai za a bayar da kudaden ne a matsayin tallafi da kuma lamuni marar ruwa, ga wasu daga cikin kasashen da suka fi fama da talauci a duniya dake nahiyar.

Shugaban Bakin duniya Jim Yong Kim ya ce kudadan za su taimakawa kasashen Afurka bunkasa da samar da ayyukan yi da kuma basu kariya daga tabarbarewar tattalin arzikin kasashen waje dama rikice-rikice.

Za a samo dala biliyan 45 daga cikin dala biliyan 57 din ne daga kungiyar bunkasa kasashe wadda wani bangare ne na bankin duniyan na kasashen da suka ci gaba.

Kudaden za su tallafa wa ayyukan yi 400 da ake yi a kasashen Afurka kudu da Hamada kama da kuma bunkasa ababan more rayuwa kamar ilimi da samar da tsaftataccan ruwan sha da kiwon lafiya.

Manufar hakan dai shi ne a samar da yanayin bunkasa tattalin arzikin kasashen. Faduwar farashin kayayyakin da aka samu a 'yan shekarun nan ya matukar shafar yankin, to amma dai ana sa ran kyautatuwar yanayin a wannan shekarar.

Masu lura da al'amura sun ce wannan yunkurin na bankin duniya zai tallafa wajan dorewar ci gaban da ake sa ran samu.