Amurka za ta hana kasashe 8 shiga jirgi da kwamfuta

A Transportation Security Administration (TSA) officer reads the X-ray of a laptop computer at Baltimore-Washington International Airport. Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Sabon matakin zai shafi kamfanin jiragen kasashe 13

Amurka za ta haramtawa wasu kasashe takwas na yankin Gabas ta Tsakiya da Kudancin Afirka, shiga jirage masu zuwa kasar da kayayyakin wuta irin su kwamfuta.

Wata majiya daga gwamnatin Amurka ta shaida wa BBC cewa, matakin zai shafi kamfanin jirage guda tara ne wadanda suke jigila a filayen jiragen saman kasar.

Kafofin yada labaran Amurka sun ruwaito cewa, an dauki wannan mataki ne saboda bayanan sirri da aka samo daga wasu kasashe.

An kuma ruwaito cewa matakin zai hada ne da haramta shiga da kayayyaki kamar kwamfutoci da kyamarori da na'urar bidiyo ta DVD da na'urar yin gem, amma ban da wayoyi.

Hukumar kula da tsaron cikin gida ta Amurka, ta ki cewa komai a kan lamarin, amma ana sa ran za ta gabatar da jawabi a ranar Talata.

Ita ma hukumar Tsaro ta bangaren Sufuri ta ki tofa komai kan lamarin.

Har yanzu ba a fitar da jerin sunayen kamfanonin jiragen kasashen da matakin zai shafa ba, amma wani jami'i ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AP cewa, lamarin zai shafi jiragen da ke tasowa daga filayen jirgi 10 ne daga kasashe takwas kamar haka:

  • Filin jirgin Queen Alia da ke birnin Amman, a Jordan
  • Babban filin jirgin saman Alkahira da ke Masar
  • Filin jirgin sama na Ataturk na birnin Istanbul a Turkiyya
  • Babban filin jirgin sama na Sarki Abdulaziz da ke Jeddah a Saudiyya
  • Babban filin jirgin sama na Sarki Khalid da ke Riyadh a Saudiyya
  • Babban filin jirgin sama na Kuwait
  • Filin jirgin sama na Mohammed V, da ke Casablanca a Moroko
  • Filin jirgin sama na Hamad da ke Doha a Qatar
  • Babban filin jirgin sama na Dubai a kasar Hadaddiyar Daular Larabawa
  • Filin jirgin sama na Abu Dhabi a kasar Hadaddiyar Daular Larabawa

Jami'ai sun ce matakin ba shi da ranar karewa. Kamfanin AP ya ruwaito cewa ba a sanar da kamfanin jiragen saman a hukumance ba har sai da misalin karfe bakwai na safiyar Talata agogon GMT.

Sai dai kamfanin jirgin sama na Jordan ya rubuta a shafinsa na Twitter cewa, zai haramtawa fasinjoji shiga jiragensa masu zuwa Arewacin Amurka da kayan lantarki, kamar yadda kafar yada labarai ta CNN ta fara ruwaitowa.

Sai dai daga baya an goge rubutun.

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Waiwaye

A watan Fabrairun 2016 ne bam ya fashe a wani jirgin kasar Dubai na kamfanin Daallo, jim kadan bayan tashinsa daga Mogadishu, babban birnin kasar Somaliya.

Masu bincike sun ce wani fasinja ne ya shiga da wata kwamfuta mai dauke da bam. Matukin jirgin dai ya yi azamar tsayar da jirgin, kuma aka yi sa'a wanda ake zargi da shiga da bam din ne kawai ya mutu.

An yi hasashen cewa da a ce a lokacin da bam din ya fashe jirgin yana zura gudu ne a sararin samaniya, to da ba abin da zai hana jirgin tarwatsewa a sama.

Kungiyar Al-Shabab mai alaka da al-Qaeda ce ta dauki alhakin kai harin.

Sai dai kuma da yake ana kaffa-kaffa kan abin da ya shafi bayanan sirri, jami'ai suna sanyi-sanyi wajen samo cikakken bayani a kan dalilin da ya sa Amurka ta gabatar da wannan sabon mataki.

Labarai masu alaka