Kotu ta bayar da belin Andrew Yakubu

Andrew Yakubu
Image caption Andrew Yakubu tsohon shugaban hukumar man fetur ta Najeriya ne

Wata babbar kotu a Abuja, ta bayar da belin tsohon shugaban kamfanin man fetur na Najeriya, NNPC, Andrew Yakubu.

Kotun ta bayar da belinsa ne a kan naira miliyan 300, ya kuma gabatar da mutum biyu da za su tsaya masa, daya daga cikinsu ya kasance ya mallaki gida a Abuja, babban birnin kasar, yayin da dayan kuma ya kasance yana da gida a ko ma ina ne a Najeriya.

Mai shari'a AR Mohammed wanda ya jagoranci zaman kotun a ranar Talata, ya ce dole mutane biyun da za su tsaya masa, su bayar da fasfo dinsu ga kotun.

Haka kuma alkalin ya bukaci Mista Andrew ya bayar da nasa fasfo din ga kotun, an kuma hana shi yin bulaguro zuwa ko wacce kasa.

Ibrahim Bawa na daya daga cikin lauyoyi goma 12 da ke kare Mista Andrew, ya kuma shaida wa BBC cewa za a yi kokarin cika ka'idojin a yau.

Ya ce abin da ake nufi da bayar da naira miliyan 300 a matsayin kudin beli, shi ne, "Ba wai kudin za a bayar ba, ana nufin idan har bai dawo kotu ba a zama na gaba, to wanda ya karbi belinsa ne zai zo ya biya wannan kudin."

Mai shari'a AR Mohammed dai ya dage zaman kotun zuwa 9 ga watan Mayun 2017.

Ana dai tuhumar Mista Yakubu ne da laifufuka guda shida da suka hada da boye wasu makudan kudi a gidansa, to sai dai ya masunta dukkan tuhume-tuhume guda shida da ake masa.

A watan da ya gabata ne hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC, ta kama Mista Yakubu, sakamakon gano miliyoyin daloli a wani gidansa a Kaduna.

Labarai masu alaka