'Yan takarar Faransa sun yi sa'insa kan sanya burkini

'Yan takara Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Francois Fillon da Emanuel Macron da Benoit Hamon da Jean-Luc Melenchon da kuma Marine Le Pen kafin muhawarar

Manyan 'yan takara biyu da ke yakin neman zaben shugaban kasar Faransa sun yi sa'insa mai zafi a muhawarar da suka yi a talabijin, a karon farko.

'Yan takara Marine Le Pen da Emanuel Macron sun tabta muhawara a kan sanya kayan ninkaya da ke rufe jiki ruf wato Burkini, da mata Musulmai ke amfani da su.

Ms Le Pen ta ce kamata ya yi a kawo karshen cudanyar al'adu, inda Mista Macron ya zargeta da zama makiyyar Musulmai a Faransa.

Mista Fillon ya ce idan ya lashe zabe, zai zama shugaban kasar da zai mayar da kasar yadda take a da.

Inda ya kara da cewa sanya burkini al'amari ne na jama'a kuma ba kalubale ba ne ga al'adar Faransa, kamar yadda Ms Le Pen ta fada.

Wurin shakatawa da dama a kudancin Faransa sun dakatar da sanya burkini kafin babbar kotun kasar ta yanke shawarar cewa yin hakan take hakkokin dan adam ne.

Masu bayar a shawara a zaben kasar na hasashen cewa Ms Le Pen za ta yi nasara a zagaye na farko, amma Mista Macron zai kayar da ita a zagaye na biyu.

Sauran 'yan takara uku a muhawarar da aka gudanar a ranar Litinin sun hada da Mista Francois Fillon da Mista Benoit Hamon da Mista Jean-Luc Melenchon.

Muhawarar ta mayar da hankali ne a kan manyan al'amuran da suka shafi kasar kamar ayyukan yaki da ta'addanci da kuma matsayin Faransa a Turai.

Kallon Muhawar a Paris - Sharhin wakilin BBC

Zai yi wuya a canki wanda ya lashe muhawarar. Dukkan 'yan takarar sun yi kokari, sun bayyana manufofinsu, don hakan ya saura ga al'ummar kasar su yanke hukunci.

A nawa tunanin, na farko Mista Emmanuel Macron ya yi kokari, idan har wasu na ganin ba zai yi kokari ba, to basu canka daidai ba.

Ms Marine Le Pen ba ta yi kokari yadda ake zato ba. Magoya bayanta ba za su damu da hakan ba.

Amma sai dai duk dan takarar da ya yi nasara, dole ne ya ajiye bambanci ya tafi da kowa, abin da ake ganin Miss Le Pen ba zata iya yi ba.

Mista Francois Fillon bai yi kokari ba. Ya kasance kamar wasu lokutan kamar baya cikin masu muhawarar.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption 'Yan takarar, Francois Fillon da Benoit Hamon da Marine Le Pen da Emmanuel Macron da Jean-Luc Melenchon

A lokacin muhawarar Mista Macron ya ce zai sauya bambancin da ke siyasar kasar, yayin da Ms Le Pen ta dauki alkawarin za ta dauki mataki sosai a harkar shige da ficen kasar.

Ana bincike a kan zargin cewa Mista Fillon ya biya matarsa dubban Euro na aikin majalisa da bata yi ba.

Zargin da Mista Fillon ya musanta kuma ya ki ya sauka daga yakin neman zabe, inda ya ce wannan bita da kullen siyasa ne.

'Yan takarar sun tabka muhawara akan yadda za a magance rashin aikin yi.

Al'ummar kasa zasu jefa kuri'a rana 23 ga watan Afrilu.

Labarai masu alaka

Karin bayani