Kamaru na ci gaba da korar 'yan gudun hijirar Nigeria

Najeriya Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Dubban yan Najeriya na gudun hijira a Kamaru

Majalisar dinkin duniya ta ce Kamaru na tursasawa dubban 'yan gudun hijirar Najeriya, wadanda rikicin Boko Haram yasa suka kaura da su koma gida.

Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta majalisar dinkin duniya ta ce, ya zuwa yanzu, rundunar kasar ta mayar da sama da mutum 2,600 zuwa wasu kauyuka dake arewa-masogabashin Najeriya.

Hukumar ta ce kauyukan na fama da rashin isashen abinci kuma rashin tsaro na cigaba.

A farkon watan nan ne kasashen biyu suka saka hannu a wata yarjejeniya dake cewa ba za a tilastawa 'yan gudun hijira komawa kasashensu ba.

Sama da 'yan gudun hijirar Najeriya 85,000 ne ke zama a yankin arewa mai nisa na Kamaru.

A nan ne kungiyar Boko Haram ke yawan kai hare-haren da suke amfani da mata 'yan kunar bakin wake da kuma yara.

Hare-haren 'yan kungiyar Boko Haram ya yi sanadiyar mutuwar dubban mutane, ya kuma raba dubun dubatar mutane da muhallansu a yankin arewa maso Gabashin Najeriya.

Labarai masu alaka